Anthony Seibu Alec Abban
9 ga Yuni, 1965 - 24 ga Faburairu, 1966 Election: 1965 Ghanaian parliamentary election (en)
1956 - 1965 Election: 1956 Gold Coast legislative election (en)
15 ga Yuni, 1954 - 17 ga Yuli, 1956 Election: 1954 Gold Coast legislative election (en) | |||||||
| Rayuwa | |||||||
| Haihuwa | Kogin Zinariya (Mulkin mallaka na Birtaniyya), 4 ga Yuni, 1928 | ||||||
| ƙasa | Ghana | ||||||
| Mutuwa | 2 Oktoba 1985 | ||||||
| Karatu | |||||||
| Makaranta |
Makarantar Mfantsipim Kwalejin Ilimi ta Wesley, Kumasi Teachers' Training Certificate (en) | ||||||
| Sana'a | |||||||
| Sana'a | ɗan siyasa da minista | ||||||
| Imani | |||||||
| Addini |
Kiristanci Kirista | ||||||
| Jam'iyar siyasa |
Convention People's Party (en) | ||||||
Anthony Seibu Alec Abban malami ne kuma ɗan siyasa ɗan kasar Ghana. Ya kasance ɗan majalisa a jamhuriya ta farko. Ya fara zama ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ajumako-Asikuma daga shekarun 1954 zuwa 1965. A shekarar 1965 aka raba mazaɓar kuma ya zama ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ajumako. Ya kuma kasance mataimakin minista a muƙamai daban-daban a jamhuriya ta farko. A jamhuriya ta uku, ya kasance memba na jam'iyyar People's National Party, jam'iyyar da ta ci zaɓen shekara ta 1979. Abban malami ne mai horarwa. Kafin shiga siyasa, ya koyar a makarantu daban-daban a lokacin Gold Coast.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Abban ranar 4 ga watan Yuni 1928. Ya yi karatun sa na farko a Makarantar Methodist Ajumako. Ya ci gaba a makarantar Mfantsipim inda ya ci jarrabawar kammala karatunsa na London a shekarar 1948. Ya wuce Kwalejin Wesley da ke Kumasi inda ya samu takardar shaidar 'A' na Malami.
Aiki da siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Kafin siyasa Abban ya koyar a makarantu a Winneba da Odoben duk a yankin tsakiyar Ghana. A shekarar 1954 aka zaɓi Abban a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar Ajumako-Asikuma. Yayin da yake majalisar ya riƙe muƙamin mataimakin minista a ma'aikatu daban-daban, wasu daga cikinsu sun haɗa da ma'aikatar masana'antu, da ma'aikatar noma. [1] A shekarar 1965 ya zama ɗan majalisa Ajumako lokacin da aka raba mazaɓar sa. Ya yi wannan aiki har zuwa shekara ta 1966 lokacin da aka hambarar da gwamnatin Nkrumah.
A jamhuriya ta uku Abban ya shiga jam’iyyar People’s National Party kuma yana ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar. [2]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Abban ya rasu a ranar 2 ga watan Oktoba 1985 yana da shekaru 57. [3]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jerin 'yan majalisar da aka zaba a zaben majalisar dokokin Gold Coast na 1954
- Jerin 'yan majalisar da aka zaba a zaben majalisar dokokin Gold Coast na 1956
- Jerin sunayen 'yan majalisar da aka zaba a zaben 'yan majalisar dokokin Ghana na 1965
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Ghana Year Book". Graphic Corporation. 1962. p. 12.
- ↑ "Ghana News, Volumes 8–12". Washington, D.C. : Embassy of Ghana. 1979. p. 5.
- ↑ "West Africa, Issues 3600–3616". West Africa Publishing Company Limited. 1986. p. 2126.