Jump to content

Apollonia Mathia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Apollonia Mathia
Rayuwa
Haihuwa 1950s
ƙasa Sudan ta Kudu
Mutuwa Juba, 18 ga Maris, 2011
Sana'a
Sana'a ɗan jarida da gwagwarmaya

Apollonia Mathia (ta mutu a ranar 18 ga watan Maris na shekara ta 2011) 'yar jaridar Sudan ta Kudu ce kuma mai gwagwarmayar kare hakkin bil'adama. Mathia na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Ƙungiyar Mata ta Media dake Sudan ta Kudu (AMWISS) da kuma Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Kudancin Sudan (UJOSS).

Tarihin ta da karatun ta

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mathia a shekarar 1950s. Tayi yaran tarta a northern Uganda kafin ta koma Juba.[1][2]

Kafin ta fara aiki a Ma'aikatar Kudi a matsayin sakatariya a 1978, Mathia ta yi aiki a matsayin Manajan Bayanai a Cocin Katolika. Daga baya ta bar aikin don shiga Juba Post inda ita ce kadai edita mace da Manajan edita. Ta bar Juba Post a shekara ta 2008 kuma ta fara aiki da BBC Monitoring Service a matsayin wakiliyar su a Sudan ta Kudu. [3][1]

Mathia ta yi aiki a ma'aikatu da dama kuma ta taimaka wajen kirkiran kungiyar 'yan jarida ta Kudancin Sudan (UJOSS). Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara a sashen saka hannun jari na Bankin Duniya na Sudan ta Kudu. [4]

A lokacin mutuwarta a shekara ta 2011, Mathia ta kasance Babban Darakta na Ƙungiyar Mata ta Media a Sudan ta Kudu (AMWISS) wanda ta taimaka wajen kafuwar sa shekara ta 2008 tare da Veronica Lucy Gordon da sauransu [2]

A ranar 18 ga watan Maris na shekara ta 2011, Mathia ta mutu sakamakon hatsari lokacin da babur da take Kai ya ragargaje ta hanyar babbar mota.

  1. 1 2 "Apollonia Mathia: A rock of Sudanese journalism". The Journalist. 30 April 2021. Retrieved 2022-03-21. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":2" defined multiple times with different content
  2. 1 2 "Remembering South Sudan's pioneer female reporter". Committee to Protect Journalists (in Turanci). 30 March 2011. Retrieved 2022-03-22. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":3" defined multiple times with different content
  3. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :1
  4. "South Sudan's veteran female journalist passes on". Media Diversity Institute (in Turanci). 4 April 2011. Retrieved 2022-03-22.