Jump to content

Arvo Salo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Arvo Salo
member of the Parliament of Finland (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Merikarvia (mul) Fassara, 2 Mayu 1932
ƙasa Finland
Mutuwa Merikarvia (mul) Fassara, 9 ga Yuli, 2011
Karatu
Harsuna Finnish (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, marubin wasannin kwaykwayo, ɗan jarida da marubuci
Wurin aiki Helsinki
Kyaututtuka
Imani
Jam'iyar siyasa Social Democratic Party of Finland (en) Fassara
IMDb nm0758824

Arvo Jaakko Henrikki Salo (2 Mayu 1932 - 9 Yuli 2011) marubuci ne ɗan ƙasar Finland, ɗan jarida kuma ɗan siyasa. Ya yi aiki a matsayin dan majalisa daga 1966 zuwa 1970 da kuma daga 1979 zuwa 1983 (Social Democratic Party) kuma ya kasance ministan ilimi da al'adu daga 1982 zuwa 1983 a majalisar ministoci ta uku ta Kalevi Sorsa.[1]

Bugu da kari, ya rike mukamai daban-daban na amana, wadanda suka hada da Majalisar birnin Helsinki, Gidauniyar Väinö Tanner da Kungiyar Ilimin Ma’aikata. Ya sami lambar girmamawa ta farfesa a 2003 kuma ya kasance mai karɓar lambar yabo ta Eino Leino a 1964.

A cikin siyasar Finnish an san Salo da furucinsa na "kashe wani baƙauye ɗaya kowace rana" lokacin da yake magana game da manufofin noma na Finnish.[2]

An haifi Salo kuma ya mutu a Merikarvia, Satakunta. A aikinsa na jarida, ya kasance babban editan Yliopplaslehti. Ya karɓi lambar yabo ta ɗan jarida Suomen Kuvalehti a cikin 1977. Ya rubuta manyan wasannin kwaikwayo da yawa, ciki har da Lapualaisooppera (1966), Mustalaisoperetti (1969), Yks perkele, yks enkeli (1985), Vallan miehet (1986), da Ouraooppera (2002).

opera Matilda Roslin da Nikolai, bisa ga rayuwar Roslin, Arvo Salo daga Merikarvia da mawaki Ilkka Kuusisto ne suka shirya shi.[3]

  1. Eduskunta
  2. Täysistunnon pöytäkirja PTK 42/2006 vp.
  3. "Etusivu". kansallisbiografia.fi. Retrieved 2023-09-18