Jump to content

Asanterabi Zephaniah Nsilo Swai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Asanterabi Zephaniah Nsilo Swai (1925-1994) ɗan siyasan Tanzaniya majagaba ne na al'adun Chagga.

  • Daga shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da biyu 1952 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da hudu 1954 ya kasance mataimakin mai gadi a jami'ar Makerere.
  • Daga shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da takwas 1958 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin 1960 ya kasance babban manaja, Meru Cooperative Union kuma shi ne shugaban lardin Tanganyika African National Union (TANU) na lardin Arewa.
  • Daga shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin 1960 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyu 1962 ya kasance shugaban kwamitin tattalin arziki da ci gaban zamantakewa ta TANU.
  • Daga shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyu 1962 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da bakwai 1967 ya kasance ma'ajin kasa TANU. A shekarar alif dubu daya da tara da sittin 1960 aka nada shi memba na majalisar dokoki.
  • Daga shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin 1960 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da daya 1961 ya kasance Ministan Kasuwanci da Masana'antu.
  • Daga Janairu zuwa Maris shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyu 1962 ya kasance Ministan Lafiya da Kwadago.
  • Daga Yuli zuwa Disamba shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyu 1962 ya kasance Minista ba tare da Fayil ba kuma wakilin dindindin na Tanzaniya a Majalisar Dinkin Duniya.
  • Daga shekarar alif dubu daya da dari tara sitting da biyu 1962 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da uku 1963 ya kasance ministan tsare-tsare na raya kasa Tanganyika.
  • A shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyu 1962 Nelson Mandela ya kasance bakonsa.
  • Daga shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da hudu 1964 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyar 1965 ya zama Ministan Kasa, Daraktan Tsare-tsare na Ofishin Shugaban kasa.
  • A ranar sha’uku 13 ga watan Oktoba, shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyar 1965 ya yi jawabi a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya na 1360.
  • Daga Satumba 1965 zuwa Maris 1967, ya kasance Ministan Masana'antu, Ma'adinai da Makamashi.
  • Daga Maris 1967 zuwa Yuni 1967, ya kasance Ministan Harkokin Tattalin Arziki da Tsare-tsare na Raya Kasa kuma shugaban Hukumar Raya Kasa.
  • A shekarar 1967 ya zama ministan harkokin gabashin Afrika.
  • Daga 1967 zuwa 1968 ya kasance Ministan Sadarwa, Bincike da Ayyukan Jama'a na Gabashin Afirka kuma memba a Majalisar Dokokin Gabashin Afirka.
Sakataren harkokin wajen Burtaniya mai kula da mulkin mallaka, Iain Macleod, a rana ta biyu ta ziyararsa ta farko a Tanganyika, 18 ga Disamba, 1959, ya gana da ministocin gwamnatin Tanganyika da shugabannin siyasa. Dama zuwa hagu, layi na gaba: Ernest Albert Vasey, Ministan Kudi; Mista John Fletcher-Cooke, Mataimakin Gwamna; Richard Turnbull (gwamnan mulkin mallaka), Gwamnan Tanganyika; Iain Macleod; Julius Nyerere; jere na baya: John Sydney Richard Cole, Babban Lauyan Gwamnati, [1] William Bonnar Leslie Monson (1912–1993), Ƙarƙashin Sakatare, Ofishin Mulki; na gaba biyu ba a sani ba; a dama, a bayan Julius Nyerere, Mista Nsilo Swai (daga baya minista),

Bayanan da aka ambata

[gyara sashe | gyara masomin]