Jump to content

Asinansi Nyakato

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Asinansi Nyakato
member of parliament (en) Fassara

2021 -
Rayuwa
Haihuwa Hoima District (en) Fassara, 
ƙasa Uganda
Karatu
Makaranta Jami'ar Ndejje
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Asinansi Nyakato, wacce aka fi sani da Kamanda, 'yar siyasa ce a ƙasar Uganda, kuma 'yar majalisar dokoki ce ta birnin Hoima, a majalisar dokoki ta 11 daga shekarun 2021 zuwa 2026. Tana da alaƙa da jam'iyyar Forum for Democratic Change (FDC). [1] [2]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Nyakato gimbiya ce ta masarautar Bunyoro Kitara. Tana da digirin farko a fannin aikin zamantakewa daga Jami'ar Ndejje. [3]

Nyakato 'yar takarar haɗin gwiwa ce ta jam'iyyar adawa. A shekarar 2011, ta tsaya takarar kujerar 'yan majalisar mata ta Hoima kuma ta fito a matsayin ta biyu bayan ta sha kaye a hannun Ms Tophas Kaahwa Byagira. A watan Agusta na shekarar 2011, ta shiga Majalisar Dokokin Uganda, inda ta yi aiki a matsayin mai nazarin manufofi har zuwa shekara ta 2016. Ita 'yar Majalisar Zartarwa ce ta Ƙasa ta FDC inda take aiki a matsayin sakatariya a ayyukan kiwon lafiya. Ita ce kuma babbar sakatariya ta FDC Hoima Municipality. Ta taɓa yin aiki a matsayin sakatariya a ƙungiyar matasa ta FDC. [4] [3] Daga baya ta koma fafutukar kare al'ummomin da ci gaban mai da iskar gas ya shafa a yankin Albertine. [3]

  1. "Asinansi Nyakato Kamanda, Aspiring Woman MP 2021–2026, Hoima district". www.ugandadecides.com (in Turanci). Archived from the original on 17 April 2021. Retrieved 16 April 2021.
  2. Mulengera (23 August 2019). "FDC'S NYAKATO IS OUR HOIMA CANDIDATE TOO, P'PLE POWER – mulengeranews.com" (in Turanci). Retrieved 16 April 2021.
  3. 1 2 3 "PROFILES: Who is who in the Hoima Woman MP by- election?". PML Daily (in Turanci). 2019-09-24. Retrieved 2022-03-03.
  4. Writer, JAVIRA SSEBWAMI | PML Daily Staff (19 August 2019). "FDC picks Nyakato Asinansi for Hoima Woman MP by- election". PML Daily (in Turanci). Retrieved 16 April 2021.