Asisat Oshoala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Asisat Oshoala
Asisat Oshoala 20190421 (cropped).jpg
Rayuwa
Haihuwa Ikorodu, 9 Oktoba 1994 (25 shekaru)
ƙasa Nijeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Itinerary
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Flag of None.svg FC Robo2009-2013
Flag of None.svg Nigeria women's national football team2011-201161
Flag of None.svg Rivers Angels F.C.2013-2015
Flag of None.svg Liverpool L.F.C.2015-2015123
Flag of None.svg Arsenal W.F.C.2016-201630
Flag of None.svg Dalian Quanjian F.C.2017-2018
Flag of None.svg FC Barcelona Femení2019-23
 
Muƙami ko ƙwarewa forward Translate
Tsayi 172 cm
Kyautuka
Imani
Addini Musulunci
asisatoshoala.me

Asisat Lamina Oshoala MON (an haife shi a 9 ga watan Oktoba 1994) Yar'Najeriya ce, kuma ƙwararriyar yar'wasan ƙwallon ƙafa wacce take buga wasa a ƙungiyar FC Barcelona Femení a ƙasar Spaniya a Primera División amatsayin yar'wasan gaba.[1] Tazama mafi yawan cin ƙwallaye a gasar cin kofin duniya 2014 FIFA U-20 Kofin Duniya na mata kuma itace yar'wasa mafi ƙayatarwa. Ta sake zama yar'wasa mafi ƙayatarwa kuma nabiyu a yawan cin ƙwallaye da ƙungiyar Super Falcons wanda suka lashe gasar 2014 African Women's Championship.

Matakin Kulub[gyara sashe | Gyara masomin]

A 23 ga watan Janairun shekara ta 2015, Oshoala ta koma Liverpool Ladies. Maikula da ƙungiyar Liverpool, Matt Beard ta bayyana ta amatsayin "ɗaya daga cikin mafiya ƙayatarwan yan'wasa matasa na duniya".[2] Dukda cewa ansamu jita-jita a lokacin na zata koma ne wasu ƙungiyoyin, amma tace taji ɗadin data koma Liverpool.[3]

Oshoala tayi rashin watanni biyu na kakar 2015 sakamakon raunin gwiwa data samu, amatsayin Liverpool waɗanda Duke rike da kofin gasar amma sun ƙare amatsayi na bakwai ne cikin ƙungiyoyi takwas.[4] A watan Janairu na 2016 Liverpool ta fidda wani rehoton cewan Arsenal Ladies sun fara tattaunawa akan sayan Oshoala sannan kuma ita yar'wasan tana tattaunawa da kulub ɗin na London.[5][6]

A 10 ga watan Febrerun 2017, ƙungiyar ƙasar Sin Dalian Quanjian F.C. sun sayi Oshoala.[7]

Amma kuma a 31 Janairun 2019, ƙungiyar kasar Spaniya, FC Barcelona Femení sun sayi Oshoala akan aro na zuwa karshen ahekara.[8]

Rayuwarta[gyara sashe | Gyara masomin]

Oshoala takasance tayi matuƙar ɓata wa mahaifanta rai sanda tabar makaranta ta koma buga wasan ƙwallon ƙafa.[9] Oshoala takasance Musulma ce, Dan kuwa iyayen ta dukkaninsu mabiya addinin musulunci ne.[10]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. "Oshoala off to China". SuperSport. 11 February 2017. Retrieved 11 February 2017. 
  2. "Asisat Oshoala: Liverpool Ladies sign Nigerian prospect". BBC Sport. 
  3. Kessel, Anna (21 March 2015). "Happiness lies with Liverpool for Nigerian superstar Asisat Oshoala". The Guardian. 
  4. Currie, Jo (13 October 2015). "Liverpool Ladies: Injuries 'impacted' on season, says Beard". BBC Sport. 
  5. "Nigerian striker Oshoala to hold talks with Arsenal". Liverpool L.F.C. 26 January 2016. Retrieved 26 January 2016. 
  6. "Liverpool Ladies Accept Arsenal's Bid For Asisat Oshoala | Wolexis Sports Blog". www.wolexis.com. 
  7. sina weibo (in Chinese). Dalian Quanjian Official Weibo. 10 February 2017 http://weibo.com/ttarticle/p/show?id=2309404073755101021908 |url= missing title (help).  Unknown parameter |script-title= ignored (help)
  8. https://www.vanguardngr.com/2019/01/asisat-oshoala-joins-barcelona-from-dalian-quanjian/amp/
  9. Taylor, Louise (5 June 2015). "Women’s World Cup 2015: 10 players to watch". The Guardian. Retrieved 5 June 2015. 
  10. Wejinya, Sammy (25 October 2014). "Q & A with Asisat Oshoala". SuperSport. Retrieved 15 November 2014.