Jump to content

Ateke Tom

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ateke Tom
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a

Ateke Tom shugaba ne na gargajiya kuma ya kasance shine wanda ya fara riƙe matsayin Amanyanabo a daular 'Okochiri', kuma ya kasance tsohon shugaban 'yan sintiri ne na Nija Delta, haka zalika ya kasance daga cikin sojojin sa-kai na yaren Ijaw dake yankin Nija Delta a Nijeriya. [1]A shekara ta 2007 a lokacin fada tsakanin sojojin sa-kai da hukumar bada tsaro a jihar Patakwal, Ateke Tom ya rubuta takarda zuwa ga gwamna, Celestine Omehia, don sasanci akan dama da gwamnatin ta bada na yafiya ga duk dan tawaye ko sojin sa-kai da ya miqa kanshi.[2]

A ranar 25, ga watan Nuwamban shekarar 2017, an nada Ateke Tom a matsayin Amanyanabo na farko a Okirichi. Taron nadin ya samu halartar Ezenwo Wike, gwamnan jihar Rivers.

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2009-10-04. Retrieved 2021-05-17.
  2. https://www.legit.ng/1137318-former-militant-leader-ateke-tom-crowned-king-niger-delta.html