Austin Akobundu
| Rayuwa | |
|---|---|
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
Austin Akobundu ɗan siyasan Najeriya ne wanda shine Sanata mai wakiltar Abia ta tsakiya.[1]
Tarihin Rayuwarsa
[gyara sashe | gyara masomin]Austin dai tsohon Kanar ne mai ritaya na sojojin Najeriya kuma tsohon ƙaramin ministan tsaro a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan[2]. Shine Sanata mai wakiltar Abia ta tsakiya a majalisar dattawa a wannan jamhoriyyar. Ya maye gurbin Darlington Nwokocha wanda kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓensa a ranar 4 ga Nuwamban shekara ta 2023. An rantsar da shi ranar 15 ga watan Nuwamba, 2023.[3][4]
Tun lokacin da Akobundu ya isa majalisar dattijai, ya kasance mai himma wajen tallafa wa harkokin ilimi, kuma kwanan nan ya samar da tallafin karatu ga ɗalibai 113 a fadin kananan hukumomin jihar Abia tare da horas da dalibai 400 kan ilimin kwamfuta a Umuahia, jihar Abia.[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Nwosu, Uche (2022-05-24). "Col. Akobundu Emerges PDP Flag Bearer For Abia Central Senatorial District". Independent Nigeria. Retrieved 2024-03-06.
- ↑ "Ex-minister joins race for Abia senatorial seat". The Punch. 2022-03-31. Retrieved 2024-03-06.
- ↑ Ogundapo, Abdulqudus (2023-11-15). "New Abia Central senator sworn in". Premium Times. Retrieved 2024-03-06.
- ↑ Ume-Ezeoke, Gloria (2023-11-15). "PDP's Akobundu Sworn In As Abia Senator". Channels TV. Retrieved 2024-11-11.
- ↑ Nwosu, Uche (2024-08-30). "FG, Senator Akobundu Foundation Train Over 400 Students In Computer Software In Umuahia". Independent Nigeria. Retrieved 2024-11-11.