BOC Madaki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
BOC Madaki
Rayuwa
Cikakken suna Luka Bulus
Haihuwa Jihar Bauchi, 22 Satumba 1993 (30 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a mai rubuta waka, Masu kirkira da rapper (en) Fassara
Imani
Addini Kiristanci

Luka Bulus Madaki; wanda aka fi sani da BOC Madaki (An haifeshi ranar 22 ga watan Satumban shekarar 1993)[1] ɗan Najeriya ne, Marubucin Waƙa, Kuma mawaƙi.

Rayuwar farko da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi shine ranar 22 ga watan Satumban shekarar 1989 a ƙaramar hukumar Bogoro da ke Jihar Bauchi a matsayin ɗan fari ga iyayensa.

BOC yayi karatunsa na firamare a makarantar gandun daji da Jibril Aminu kafin ya zarce zuwa makarantar sakandaren kwana ta Shadawanka inda ya samu shedar SSCE.

Bayan ya kammala makarantar sakandare, ya kuma cigaba zuwa makarantar kimiyya da fasaha ta Abubakar Tatari Ali inda ya sami difloma ta ƙasa a fannin nazarin muhalli da kula da gidaje.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Ayyukan sa na waƙa ya fara ne daga Coci tare da ƙaramin rukuni na mawaƙa, bayan shafe shekaru yana gwagwarmaya a cikin waƙa, ƙarshe BOC Madaki ya ci gaba a shekarar 2013.

BOC ya zama shahararren mawaƙi a lokacin da ƙungiyar Toss A Popular Music ta sa hannu a wancan lokacin.

Tunda ya shiga harkar waka, BOC ya fitar da wakoki sama da 100 wanda ya gabatar da manyan mawaka na hausa kamar Classiq, DJ AB, Kheengz, Morell da Bash ne pha.

Madaki ƙwararren mai waƙoƙin waƙa ne da kiɗa mai ban sha'awa, waƙoƙin sa suna mai da hankali ga canza rayuwar matasa.

Waƙoƙi[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu daga cikin wakokin sa da sukayi fice shine Zafi, Dabarbaru, da dai sauransu kuma yafitar da Album da dama kamar wane album dinshe No English, Sorry Please thanks da dai[2][3][4][5][6][7][8][9][10][11]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://naijadailys.com.ng/boc-madaki-biography-age-real-name-songs-and-net-worth/
  2. Sureplaylist.com (2020-12-27). "ALBUM: THE FOUR HORSEMEN EP – DJ AB x Kheengz x Deezell x B.O.C Madaki". Sureplaylist. Archived from the original on 2021-05-20. Retrieved 2021-05-20.
  3. NaijaDrop.com (2021-01-19). "ALBUM: B O C Madaki – Northy By Nature". Naxeer. Archived from the original on 2022-04-18. Retrieved 2022-04-18.
  4. corejamz.com (2021-01-18). "ALBUM: B O C Madaki – Northy By Nature". zadok. Archived from the original on 2021-02-20. Retrieved 2021-01-23.
  5. NaijaDrop.com (2021-08-22). "Wasu Daga Cikin Wakokin BOC Madaki". Naxeer. Archived from the original on 2022-02-14. Retrieved 2022-04-18.
  6. Naijabasic.ng (2022-02-22). "B.O.C Madaki & Odumodublvck – The Drop The Album" (in Turanci). Bala MD. Archived from the original on 2022-04-17. Retrieved 2022-04-17.
  7. Naijabasic.ng (2020-12-09). "B.O.C Madaki – Sorry,Please,Thanks The Album" (in Turanci). Bala MD. Archived from the original on 2022-04-18. Retrieved 2022-04-18.
  8. Naijabasic.ng (2021-08-27). "B.O.C Madaki – No English The Album" (in Turanci). Bala MD. Archived from the original on 2022-04-18. Retrieved 2022-04-18.
  9. Naijabasic.ng (2019-12-31). "B.O.C & C Man – Darasin Rayuwa The Album" (in Turanci). Bala MD. Archived from the original on 2022-04-18. Retrieved 2022-04-18.
  10. Naijabasic.ng (2017-12-20). "B.O.C Madaki - Ra'ayi The Album" (in Turanci). Bala MD. Archived from the original on 2022-04-18. Retrieved 2022-04-18.
  11. Naijabasic.ng (2019-01-19). "B.O.C Madaki - Allah Ya Tsare The Album" (in Turanci). Bala MD. Archived from the original on 2022-04-18. Retrieved 2022-04-18.