Jump to content

Babatunde Ayi Olatundun

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Babatunde Ayi Olatundun
Rayuwa
Haihuwa Ilorin, 12 ga Augusta, 1961 (64 shekaru)
Karatu
Makaranta Oyun Baptist High School Ijagbo (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Babatunde Ayi Olatundun mai gudanarwa ce kuma ƴar siyasa a Najeriya. Ta wakilci mazabar Ilorin ta Arewa maso Yamma, yankin karamar hukumar Ilorin ta Yamma a Majalisar Dokokin Jihar Kwara ta 10. [1][2][3]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Babatunde a ranar 12 ga watan Agustan shekara ta 1961 a Ilorin, yankin karamar hukumar Ilorin ta Yammacin Jihar Kwara Najeriya. Ta halarci makarantar sakandare ta Oyun Baptist, Ijagbo, a Oyun kuma ta sami takardar shaidan makaranta West African School Certificate a shekarar 1981. [1]

Tsakanin 1989 da 1994 ta yi aiki a matsayin jami'ar gudanarwa a Kwara State Broadcasting Services (Rediyo Kwara) da sauran kamfanoni masu zaman kansu. Ta shiga siyasa a shekarar 2014, lokacin da aka nada ta a matsayin shugabar mata ta Jam'iyyar People's Democratic Party da Buhari Support Organisation. An zabe ta a matsayin memba na majalisar dokokin jihar wanda ke wakiltar mazabar Ilorin ta Arewa maso Yamma a Majalisar Dokokin Jihar Kwara a babban zaben 2023.[1][4][5]

  1. 1.0 1.1 1.2 "HON. BABATUNDE AYI OLATUNDUN". Kwara State House of Assembly (in Turanci). Archived from the original on 2024-12-05. Retrieved 2024-12-03. Cite has empty unknown parameter: |4= (help)
  2. Azeez, Biola (2023-08-02). "Women dialogue identifies factors impeding participation in politics". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2024-12-27.
  3. "Kwara: Lawmakers call for more science teachers, laboratories in schools | Western Post" (in Turanci). 2024-11-28. Retrieved 2024-12-27.
  4. "Kwara APC Wins 23 Assembly Seats, PDP Clinches 1 – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Archived from the original on 27 December 2024. Retrieved 2024-12-27.
  5. Oyekola, Tunde (2023-03-21). "Five women get Kwara Assembly seats". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-12-27.