EmefeleGodwin Emefiele ma'aikacin banki ne a Najeriya wanda ya riƙe muƙamin gwamnan Babban Bankin Najeriya tun ranar 4 ga watan Yunin shekarar ta dubu biyu da goma sha huɗu, 2014 har zuwa 9 ga watan Yuni, 2023. An haife shi a ranar 4 ga watan Augusta shekarar ta alif ɗari tara da sittin da ɗaya, 1961 a jihar Legas ta Najeriya, Emefiele ɗan asalin Ika South ne, yankin Agbor na jihar Delta..
Rana a Venus ta fi shekara guda akan Venus? Venus tana jujjuyawa a kan kusurwarta a hankali, tana ɗaukar kwanaki 243 a duniya, amma tana ɗaukar kimanin kwanaki 225 ne kawai don kewaya rana.
Yaƙi mafi gajarta a tarihi shine tsakanin Birtaniya da Zanzibar a ranar 27 ga Agusta, 1896 Minti 38 kawai ya yi.
Ba a ganin Babbar Ganuwar Ƙasar Sin daga sararin samaniya kai tsaye? Wannan tatsuniya ce gama gari. Ƴan sama jannati, duk da haka, suna iya ganinta daga sararin samaniya.
Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin-gadi, yarjejeniyar zata fara aiki ne a ranar Alhamis 23 ga Nuwamba, 2023.
Babbar kotun Tarayyar Najeriya da ke Abuja a Najeriya ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele, kan kuɗi naira miliyan 300 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.
Wasu da ake zargin mayaƙan ƴan a-ware ne daga yankin renon Ingila na Kamaru sun kashe kimanin mutum tara a wani samame da suka kai a wani ƙauye da ke yankin yammacin kasar.
Kwanaki biyu bayan sace shugaban ƙaramar hukumar Kwali dake Abuja, Rahotanni daga birnin Tarayyar Najeriya, Abuja na cewa an yi garkuwa da wasu mata takwas a yankin Kuje.