Jump to content

Babbar Kasuwar Yamai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukala mai kyau
Babbar Kasuwar Yamai
market (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Nijar
Kasancewa a yanki na lokaci UTC+01:00
Zanen gini Kalt Pouradier-Duteil Vignal (en) Fassara
Wuri
Map
 13°30′59″N 2°07′02″E / 13.51646°N 2.11734°E / 13.51646; 2.11734
JamhuriyaNijar
BirniNiamey
Yankin babban kasuwar. Ana iya ganin ginshiƙan da ke kewaye da gine-ginen tsakiya a gefen dama na wannan hoton.

Babbar Kasuwar Niamey (Faransanci: Grand marché de Niamey) ita ce babbar kasuwa kuma cibiyar cinikayyar kasuwa a Niamey, babban birni kuma birni mafi girma a ƙasar Nijar, ƙasar da ke a Yammacin Afirka.[1]

Babbar kasuwar na a tsakiyar birnin a cikin unguwar da ake kira "Grand Marché" bayan kasuwar, gabas da kudu na tsarin kasuwanci da kuma cibiyar gwamnati ta Turai na unguwar "Plateau". An gina kasuwar a wani wurin shakatawa na zamanin mulkin mallaka wanda ya raba sassan "Turai" da "Afirka" na birnin, kudu da yammacin Stade Général Seyni Kountché na zamani da Babban Masallacin Niamey. Kasuwar tana da iyaka a yammacin Boulevard de l'Independence, wanda kuma ta nan ne a hanyar arewa maso kudu ta birnin; Route nationale 1.[2]

Tsarin Kasuwar

[gyara sashe | gyara masomin]

An fara gina shagunan kasuwancin kasuwar a shekarar 1950. Ada ana kiran kasuwar da sunan Habou-Béné'. Wata gobara da ta tashi a ranar 30 ga watan Maris, 1982 ta yi sanadiyar lalata kasuwar, daga baya an sake buɗe kasuwar a ranar 5 ga watan Janairun 1987, bayan wani aikin sake ginawa wanda ya ci kuɗi zunzurutu har CFA biliyan 5. Wannan aikin sake ginawa ya ƙunshi shaguna dubu 4000, kama daga rumfuna masu sauƙi da tebura da sauran ayyukan kasuwar; rumfunan ƙarfe zuwa shagunan zamani a cikin manyan gine-gine guda biyu.[3] A cikin watan Mayun 2009, wata gobarar ta kone wasu sassan kasuwar, inda ta lalata kusan rumfuna 1500 da tantuna.[3][4] An yi imanin cewa gobarar ta tashi ne a yankin da aka kebe rumfunan abinci. Jami’an kashe gobara sun yi zargin wata gajeriyar igiyar wutar lantarki ce ta yi silar assasa gobarar, wadda ta fara da misalin karfe 14:00, an kashe gobarar Bayan kwashe sa’o’i hudu tana ci.[5]

Ƙungiyar gwamnatin ƙasa ce ke tafiyar da rukunin kasuwar, SOCOGEM ("Société de Construction et de gestion des marchés", "Ƙungiyar Ginawa da Ayyukan Kasuwanni ta Ƙasar")[3]

Babbar Kasuwar Niamey kuma cibiyar kasuwanci ta dukan gundumar ko yankunan birnin,[6] yayin da kayayyaki daga ko'ina cikin ƙasa da ƙasashen waje ke wucewa ta cibiyar kuma ana saya gami da siyarwa. A Cibiyar sana'ar gargajiya a kasuwar ta taka rawa wurin karin jawo hankalin masu buɗe ido, tana jawo kimanin masu yawon buɗe ido kimanin dubu 20,000 a shekara.[7] Babban tashar bas da taksi suna daga bayan kasuwar.

An gina kasuwar ashekarar 1950. Gobara ta lalata kasuwar a shekara ta 1982 kuma an sake gina ta a 1987 inda sake ginin nata ya lashe zunzurutun kudi har dala biliyan 5. A yau Babbar Kasuwar tana jawo kimanin masu yawon buɗe ido mutane dubu 20,000 a kowace shekara.

  1. Fire ravages Niamey's biggest market. Sapa-AFP. May 28, 2009.
  2. Geels, Jolijn (2006). Niger. Chalfont St Peter, Bucks / Guilford, CT: Bradt UK / Globe Pequot Press. ISBN 978-1-84162-152-4.
  3. 3.0 3.1 3.2 Visite du Président de la République au Grand marché de Niamey : compassion aux sinistrés, mais fermeté à reconstruire et sécuriser le Grand marché de Niamey Archived 2012-02-20 at the Wayback Machine. Siradji Sanda, le Sahel Vendredi, 29 Mai 2009.
  4. Plusieurs boutiques consumées suite à un incendie au Grand marché de Niamey Archived 2009-05-30 at the Wayback Machine. APA news. 27 May 2009.
  5. Incendie au Grand marché de Niamey : mettre l'accent sur la prévention et la prévision, selon le commandant du 8ème groupement régional d'incendie et de sécurité Archived 2012-02-20 at the Wayback Machine. Oumarou Moussa, le Sahel. 29 Mai 2009
  6. Niger's main trade centre gutted by fire. PANA Press. 27 May 2009.
  7. INCENDIE DU GRAND MARCHÉ Des tonnes de marchandises parties en fumée. H. Adamou, Republican, Niger. 29 May 2009.

Wasu Majiyoyi

[gyara sashe | gyara masomin]

Adireshin Waje

[gyara sashe | gyara masomin]