Jump to content

Balarabe Abbas Lawal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Balarabe Abbas Lawal
Rayuwa
Haihuwa 5 ga Faburairu, 1958 (68 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Balarabe Abbas Lawal (an haife shi a ranar 5 ga watan Fabrairun shekara ta 1958) ma'aikacin gwamnati ne kuma ɗan siyasa wanda shine Ministan Muhalli na yanzu na Najeriya.[1]

Lawal ya halarci Kwalejin Barewa don karatun sakandare. Daga baya ya sami digiri na farko da digiri na biyu a kimiyyar siyasa daga Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria .

Lawal yayi aiki a matsayin Secretaryna Kaduna State Government karkashin Gwamna Uba Sani daga ranar 30 ga watan Mayun 2023 har zuwa lokacin da ya zamo Minista na Environment a watan October 2023. a baya ya rike irin wannan matsayi karkashinGwamna Nasir El-Rufai daga watan May 2015 zuwa watan Mayun 2023[2]

Ya kuma yi aiki a matsayin Shugaban Ma'aikata ga El-Rufai a lokacin da yake Ministan Babban Birnin Tarayya daga Yuli 2003 zuwa Yuli 2007.[2][3] Daga Satumba 1999 zuwa Fabrairu 2001, Lawal ya kasance Mataimakin Musamman ga Ministan Ilimi na Jiha.[4][5] Tsakanin Fabrairu 2001 da Mayu 2003, ya kuma yi aiki a matsayin Mataimakin Musamman ga Ministan Tsaro na Sojojin Najeriya.[6]

Tun da farko a cikin aikinsa, Lawal ya kasance malami a Kwalejin Nazarin Ci gaba, Zaria, daga 1982 zuwa 1989.

  1. https://www.vanguardngr.com/2023/10/what-to-know-about-abbas-lawal-balarabe-65-yr-old-ministerial-nominee-who-slumped/
  2. 1 2 https://punchng.com/seven-things-to-know-about-new-ministerial-nominee-abass-balarabe/
  3. https://newswirengr.com/2023/10/04/balarabe-abbas-lawal-biography-age-career-wife-children-achievements-net-worth-and-controversy/
  4. https://www.bbc.com/pidgin/articles/c518x2kzq0go
  5. https://leadership.ng/balarabe-halt-inauguration-group-tasks-federal-gov/
  6. https://pmnewsnigeria.com/2023/10/03/meet-balarabe-abbas-lawal-who-replaces-el-rufai-as-minister/