Bankilare
|
| ||||
| Wuri | ||||
| ||||
| Jamhuriya | Nijar | |||
| Yankin Nijar | Tillabéri | |||
| Sassan Nijar | Bankilaré Department (mul) | |||
| Babban birnin |
Bankilaré Department (mul) | |||
| Yawan mutane | ||||
| Faɗi | 84,893 (2012) | |||
| Labarin ƙasa | ||||
| Wuri a ina ko kusa da wace teku | Nijar | |||
| Altitude (en) | 277 m | |||
| Bayanan Tuntuɓa | ||||
| Kasancewa a yanki na lokaci | ||||
Bankilaré (var. Bankilare, Bankilary)[1] ƙauye ne kuma wani yanki na karkara a Nijar.[2] Garin Bankilaré, wanda ke tsakiyar garin sashen Téra Yankin Tillabéri, [1] a kusurwar arewa maso yammacin ƙasar. Garin na da nisan kilomita 60 tsakaninsa da arewacin babban birnin Téra,[3] harwa-yau wannan kwatankwacin nisa ne da shi daga iyakar Burkina Faso (zuwa yamma) da iyakar Mali (zuwa arewaci). A shekara ta 2012, ƙauyen na da yawan mutane kimanin dubu 84,893. [4]
Yawan jama'a
[gyara sashe | gyara masomin]A yankin karkarar garin Bankilaré yana da kimanin mutane 4,000 bisa alkaluman ƙididdigar shekara ta 2012, galibin mutanen ƴan ƙabilar Tuareg da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Tuareg.[5] Babbar ƙungiyar Tuareg a garin Bankilarée sune "Tenguereguedesh"[6][7] ko "Tinguereguedech", ƙungiyar Uladen Aulliminden, tsohuwar ƙungiyar zama da ke da alaka da mai daraja Kelirer Aulliminen.[8][9] Sunan "Tinguereguedech" ya samo asali ne daga kalmar yaren Tamasheq wanda ke nufin "Ina ƙarƙashin kariya na ..." Ƙarin wasu mutanen da ke zaune a karkarar sun haɗa da Loghmatten da Doufrafrak tsoffin ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Kel Ansongo Tuareg, da Fula Gaobé.[8][8]
Sauran ƙabilun da ke zaune, sun haɗa da; Songhai - mutanen Djerma, da Gourmantche . Yawan mutanen Tuareg sun fantsama zuwa sauran wurare a sashen, tare da yankin arewacin Niamey da gabashin kogin "yanki na al'adu" na Songhay.[8]
Yawancin mutanen Tuareg na yankin sun kasance asalin bayi ne a tarihi ko wasu nau'o'i masu alaƙa da hakan. Wani binciken da aka yi a shekara ta 2005 ya gano cewa "har yanzu akwai ayyukan da suka shafi bautar da bayi daga Tuareg a Bankilaré". Mutane da yawa daga wannan al'umma suna yin ƙaura zuwa yankin Abidjan.[10][11]
Tattalin Arziki
[gyara sashe | gyara masomin]Tattalin arzikin Bankilaré ya dogara ne akan kiwon dabbobi, aikin gona na gida, da kuma ayyuka ga waɗannan al'ummomin.[1] Kauyen Bankilaré sananne ne ta silar babbar kasuwar kauyen, inda ƙungiyoyi makiyaya da masu zaman kansu ke harkar saye ko siyar da kayayyaki a wannan kasuwa.[12]

Cibiyar Sadarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Bankilaré wani gari ne a lokacin rani inda makiyayan Abzinawa ke kwashe dabbobinsu. Wadannan makiyayan suna yin tafiya har ya zuwa arewacin Aljeriya. A cikin shekara ta 1999, an zaɓi garin don assasa sabon gidan rediyo. A wannan aikin na kafa gidan rediyo, mutanen garin za su samu damar aiwatar da bayanai game da filin kiwansu tare da sauran al'ummomin da ke yankin hamada. Bayan an yi nasarar aiwatar da gidan rediyon. Yanzu ƙauyen, Bankilaré kai tsaye na samun damar sadarwa ta hanyar gidan rediyo da intanet da gwamnatin Nijar da wasu ƙungiyoyi ke gudanarwa don taimaka wa mutanen isar da sakon su.[13][14][15][16][17]
Fari da karancin Abinci
[gyara sashe | gyara masomin]Garin Bankilaré ya fuskanci kalubale sosai ta fannin fari da yunwa.[18] Haka-zalika ya sake fuskantar rashin tsaro na abinci a ƙarshen shekarun 1990 da 2005.[19]
Gudanarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Bankilaré wuri ne mai mahimmanci ga makiyaya saboda yawancin makiyaya suna wucewa ko kuma suna zaune a kusa. Kafin Nijar ta samu 'yancin kai, Faransa ce ke rike da yankin. Suna da shugabanni na musamman da ake kira "Kwararrun Tuareg," kamar Michel de Geyer d'Orth, wanda ke kula da Bankilaré a 1957. Faransawa sun kafa dokoki don kula da makiyaya. Sun yi amfani da wani gari don kula da ƙungiyoyin da ake kira "Fractions" da ke yawo a yankuna daban-daban.[20] An yi amfani da wannan tsarin a wurare 27 ciki har da garin na Bankilare, tun daga shekarar 1959 a lokacin da Nijar ke ƙarƙashin mulkin mallaka daga Faransa, kuma ta ci gaba bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960. Daga baya gwamnati ta sauya yadda suke tafiyar da waɗannan yankuna, amma wasu sassa na tsohon tsarin sun dawo a karshen shekarun 1990 lokacin da yankin Bankilaré ya zama karamar hukumarsa da ake kira commune-(a kasashen da Faransa ta yi mulki karamar hukumar ana kiranta da Commune, hannu ɗaya a kasashen renon Ingila kuma aka sani da Local Government).[1][8]
Bankilaré gari ne mai ƙabilu daban-daban fiye da garuruwan da ke kusa. Kauyen na da dangantaka ta musamman da shuwagabannin gargajiya na baya, waɗanda a yanzu suke da ƙarancin tasiri a al'umma sakamakon Siyasa.[8] Bankilaré yana kusa da garuruwan da mutanen Songhay suka fi yawa, kamar Yatakala, Gorouol, da Diagourou.[8] Saboda haka, wani lokacin Bankilaré ya zama kamar ƙaramin yanki a cikin garuruwan Songhay, kuma a da ana gudanar da shi a ƙarƙashin tsarin da ake kira "Gorouol Canton,".[8] A cikin 1992, gwamnatin Nijar ta amince da Bankilaré a matsayin yanki na "Ƙungiyoyi marasa rinjaye". Tun bayan tawayen Abzinawa a cikin 1990s da kuma canje-canje a cikin ƙananan hukumomi daga 1995 zuwa 2002, tsarin kananan hukumomi ya sami matsayi na musamman na Bankilaré.[1][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 4 5 Eric Komlavi Hahonou, Mohamed Idrissa, Salou Ali. Les premiers pas de la commune de Bankilaré (an 4) Archived 2012-04-25 at the Wayback Machine: Observatoire de la décentralisation au Niger. Etudes et Travaux n° 77, Laboratoire d’études et recherches sur les dynamiques sociales et le développement local (LASDEL) Niamey. June 2009.
- ↑ Loi n° 2002-014 du 11 JUIN 2002 portant création des communes et fixant le nom de leurs chefs-lieux. Includes list of 213 communes rurales and seats, 52 Communes urbaines and seats
- ↑ Paul Stoller. Stranger in the village of the sick.
- ↑ "Bankilaré (Commune, Niger) - Population Statistics, Charts, Map and Location". www.citypopulation.de. Retrieved 2024-02-16.
- ↑ The Courier - Commission of the European Communities. Commission of the European Communities - 2002
- ↑ André Bourgeot. Horizons nomades en Afrique sahélienne: sociétés, développement et démocratie. KARTHALA Editions, 1999 ISBN 2-86537-900-0 pp.60, 65.
- ↑ Matthias Banzhaf, Boureima Drabo, Hermann Grell. From conflict to consensus: Towards joint management of natural resources by pastoralists and agro-pastoralists in the zone of Kishi Beiga, Burkina Faso Archived 2016-03-04 at the Wayback Machine. Securing the commons No.3. August 2000.
- 1 2 3 4 5 6 7 8 9 Eric Komlavi Hahonou. Une communauté nomade face à la décentralisation. In Claude Fay, Yaouaga Félix Koné (eds) Décentralisation et pouvoirs en Afrique: en contrepoint, modèles territoriaux français. Colloques et séminaires - Institut de recherche pour le développement Editions, 2006 ISBN 978-2-7099-1607-3ISBN 978-2-7099-1607-3 pp.385-406
- ↑ Hélène Claudot-Hawad. Iwellemmeden Kel Ataram (Touaregs) in Encyclopédie Berbère XXV (2003) article 176b : 3822-3828.
- ↑ Florence Boyer. L'esclavage chez les Touaregs de Bankilaré au miroir des migrations circulaires Archived 2011-08-07 at the Wayback Machine. In Cahiers d'études africaines: (2005), vol 179-180, p. 771-203.
- ↑ Boyer Florence. Initiatives captives : développement local ou invisibilité migratoire ? La migration de descendants de captifs touaregs de la zone de Bankilaré (Niger) vers Abidjan. In : Charef M. (dir.), Gonin P. (dir.) Emigrés - immigrés dans le développement local. Agadir : Sud-Contacts, 2005, p. 43-57.
- ↑ David Otto, Jonathan Otto. Niger: 2 traveler's handbook. Inter-Service Workshop, 1973. p.52
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>tag; no text was provided for refs named "fao2000". - ↑ Africa research bulletin, Volume 38, Page 14285 (Blackwell, 2001)
- ↑ Mohammed Boulahya, Macol Stewart Cerda, Marion Pratt, Kelly Sponberg. Climate, Communications, and Innovative Technologies: Potential Impacts and Sustainability of New Radio and Internet Linkages in Rural African Communities[permanent dead link]
- ↑ Rose Tchwenko. The Bankilaré Experience: An Example of a Successful Collaborative Effort to Bridge the Digital Divide Using New and Innovative Technologies.[permanent dead link].
- ↑ e-OTI: On The Internet Electronic Edition.
- ↑ Sub-Saharan Africa report - reports of Lt Col Ali Saibou's visits to stricken populations of Ayorou, Bankilaré and Nord Ouallam. United States. Foreign Broadcast Information Service. 1983.
- ↑ Southern Baptists continue relief in hungry Niger Archived 2012-04-02 at the Wayback Machine. Shawn Hendricks, International Mission Board, News & Information. 2005-08-31
- ↑ Michel de Geyer d'Orth, Les actions de développement. In Edmond Bernus (ed.) Nomades et commandants: administration et sociétés nomades dans l'ancienne A.O.F.. KARTHALA Editions, 1993 ISBN 978-2-86537-420-5 pp.127-138
Karin Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]- Pierre-Marie Decoudras. Territorialités plurielles à l'example des Touaregs de la région de Bankilaré (Niger). Les cahiers du CERVEL, Bordeaux, n° 4, 1998, pp. 143–165.
- Webarchive template wayback links
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from October 2016
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- Articles with dead external links from June 2019
- Yankin Tillabéri
- Nijar
- Pages with reference errors
- Pages using the Kartographer extension
