Barbara Allimadi
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 3 ga Yuli, 1972 |
ƙasa | Uganda |
Mutuwa | 27 ga Afirilu, 2020 |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Otema Allimadi |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Barbara Ann Allimadi (c. 1972 - 27 Afrilu 2020) 'yar siyasar ƙasar Uganda ce kuma mai fafutukar kare hakkin ɗan adam.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Allimadi a Uganda kuma mahaifinta shine Eriphas Otema Allimadi, [1] Firayim Minista na uku na Uganda (1980-1985). [2] Ɗan uwanta shine Milton Allimadi, ɗan jarida kuma wanda ya kafa jarida. [3]
Allimadi ta yi karatu a makarantar sakandare ta Gayaza, kafin danginta su tafi gudun hijira lokacin da aka hambarar da gwamnatin Obote II. [1] Ta yi karatun digiri a fannin lantarki da Injiniyanci na sadarwa a Jami'ar Metropolitan London. [4] Allimadi ta yi aikin Injiniyanci a Ingila [1] sannan ta koma Uganda a shekarar 2007. [4]
Gwagwarmaya
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar s2012, ta shirya zanga-zangar bayan Ingrid Turinawe, 'yar siyasar adawa da aka sani da "Iron Lady" na Forum for Democratic Change (FDC), [5] an ja mata nono tare da matse ta da wani jami'in 'yan sanda yayi kuma an watsa harin. Wannan ya zama sananne da "zanga-zangar mama" a Uganda. [4] Allimadi ta ce, "Na yi matukar jin haushin yadda 'yan sandan da ya kamata su kare mu sun ci zarafin wata mata a gaban kowa." [3]
Haka kuma a shekarar 2012, an kama ta bayan ta gudanar da zanga-zanga a majalisar dokokin ƙasar tare da kungiyar Concerned Citizens kuma an kwace rigarta mai ɗauke da taken yaki da cin hanci da rashawa.[6]
Allimadi ta kasance mai fafutuka na jam'iyyar siyasa ta FDC, [7] kuma a cikin shekarar 2019 ta shiga sabuwar kungiyar Alliance for National Transformation kuma ta zama sakatariyar harkokinsu na ƙasa da ƙasa, tana daidaita 'yan Uganda a cikin ƙasashen waje. [8] [2]
Mutuwa da Martaba
[gyara sashe | gyara masomin]An tsinci gawar Allimadi a gidanta da ke Kiwaatule, Kampala a ranar 27 ga watan Afrilu 2020. [9] [10] ‘Yan sanda sun buɗe bincike kan mutuwar ta. [3] [9]
An kaddamar da gidauniyar Barbra Allimadi ne domin tunawa da ita a shekarar 2021, domin bayar da tallafin karatu na kwaleji da jami’a ga ɗalibai musamman ‘yan mata. [2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 Taylor, Mildred Europa (2022-04-23). "Celebrating Barbara Allimadi, the Ugandan political activist known for her defiant bra protest". Face2Face Africa (in Turanci). Retrieved 2025-02-16. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ 2.0 2.1 2.2 Dominic, Ochola O. "Barbra Allimadi Foundation Launched in Memory of Her Freedom Fighting Legacy :". Uganda Radionetwork (in Turanci). Retrieved 2025-02-16. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":1" defined multiple times with different content - ↑ 3.0 3.1 3.2 "Ugandan Political Activist Barbara Allimadi Passes Away". OkayAfrica (in Turanci). Retrieved 2025-02-16. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":2" defined multiple times with different content - ↑ 4.0 4.1 4.2 "Barbara Allimadi". AWID. Retrieved 2025-02-16. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":3" defined multiple times with different content - ↑ "Tribute to fallen freedom fighter Barbara Allimadi". Uganda (in Turanci). 2021-05-02. Retrieved 2025-02-16.
- ↑ Watch, Human Rights (2013-02-19). World Report 2013: Events of 2012 (in Turanci). Seven Stories Press. p. 180. ISBN 978-1-60980-483-1.
- ↑ "Political activist Barbara Allimadi reported dead". Monitor (in Turanci). 2020-07-19. Retrieved 2025-02-16.
- ↑ "Allimadi hailed as justice defender". Monitor (in Turanci). 2020-07-19. Retrieved 2025-02-16.
- ↑ 9.0 9.1 "Police probe political activist Barbara Allimadi's death". Monitor (in Turanci). 2020-07-19. Retrieved 2025-02-16.
- ↑ "Neighbours' account of Allimadi's last moments". Monitor (in Turanci). 2020-07-19. Retrieved 2025-02-16.