Barkono (Kayan Dandanon Abinci)

Daga Wikipedia
A tsallaka zuwa: Shawagi, nema

Sunayen Kalma[gyarawa | Gyara masomin]

  • Barkono
  • Yaji
  • Tashshi

Asalin Kalmar[gyarawa | Gyara masomin]

Barkono kalmace wadda ake amfani da ita domin Sarrafa harshe da kuma iya amfani dashi kan ita kalmar ta rabu gidaje da dama. Kamarsu

  • Suna
  • Siffatau
  • Bayanau

Yankin Suna[gyarawa | Gyara masomin]

Barkono Sunane wanda ake amfani dashi ga wani kalar tsiro na kayan gona da lambu yanada kyawon fitowa musamman a kan kyakkyawar kasa irinsu Jigawa da kuma jangargari.

Ana noma shi mafiyawanci don samun kudi kasancewarsa mai amfani wurin dadin dandanon abinci yana da tururi da zafi idan ka ci shi da yawa a abinci ko kuma ba hadin sirki amma yana da dadin dandano da gyara abincin alfarma.

Siffatau[gyarawa | Gyara masomin]

Ana amfani da Barkono a cikin misalai dake iya zuwa a cikin jimla domin siffanta wani abu mai ban al'ajabi da kuma rashin tabbas na dabi'u domin a nuna zarra ko kuma kwazo Misali

  • Yanada Zafi Kamar Barkono
  • Shi kamar Barkono Yake a Ido
  • Banbanci Tsakanin Wuta da Barkono

kana kuma yana zuwa a cikin sigar karin magana Misali

  • Barkono a shaka da dadi amma a jika da kukan tausai