Jump to content

Bashir Zubairu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bashir Zubairu
Rayuwa
Haihuwa 28 Mayu 1968 (57 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da legislator (en) Fassara

Bashir Zubairu ɗan siyasar Najeriya ne a matakin majalisar wakilai.[1] A yanzu haka ya zama ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Birnin-Gwari/Giwa a majalisar wakilai ta ƙasa ta 10.[2] Ya ɗauki nauyin kudirori 7 tare da gabatar da kudurori da dama a majalisar dokokin ƙasar.

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Honorabul Bashir Zubairu ɗan siyasan Najeriya ne a yanzu haka yana wakiltar tarayya mai wakiltar mazaɓar Birnin Gwari/Giwa a jihar Kaduna. Ya shiga siyasa ya kuma lashe zaɓen mazaɓar sa na majalisar wakilai da kuri’u 41,023. An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai ta 10 a shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).[3]

Zubairu ya riƙe muƙamin kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna a zamanin gwamnatin Gwamna Ahmad Muhammad Makarfi, kafin ya zama majalisar. Matsayin da ya taka a majalisar dokokin jihar ya haɗa da sa ido kan ayyukan majalisa da bayar da gudummawa ga tsara manufofi a matakin jiha.

Baya ga harkar siyasa, Zubairu yana riƙe da sarautar gargajiya ta Ciroman Birnin Gwari, matsayin da ke nuna jagoranci da karɓuwar al’adu a cikin garin Kaduna.

  1. "10th National Assembly Members". orderpaper.ng. Retrieved 2024-11-25.
  2. Ogbeni, Go (2024-06-20). "Honorable members full profile: HON. ZUBAIRU BASHIR USMAN". The Green Chamber. Archived from the original on 2024-12-29. Retrieved 2024-11-25.
  3. Ogboni, Conf (2024-11-14). "Farmers lost over N100m in Kaduna maize farm attacks — Zubairu". Daily Trust. Retrieved 2024-11-25.