Bashir Aliyu Umar
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | 1961 (64/65 shekaru) |
| Sana'a | |
Dr. Bashir Aliyu Umar OON (an haife shi 27 Yuli 1961) malamin addinin musulunci ne, a Najeriya kuma shugaban majalisar koli ta shari'a a Najeriya.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Bashir ya fito daga gidan sarauta a jihar Kano mahaifinsa Hakimin Rano ne. An haifi Bashir a Kano a shekarar 1961, ya fara karatun injiniyan lantarki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya kafin ya mayar da hankali kan ilimin addinin Musulunci, inda ya samu digiri a Jami'ar Musulunci ta Madinah. Ya ƙware a fannin ilimin Hadisi inda har ya kai matsayin farfesa a fannin Hadisi, Malami ne a Jami'ar Bayero Kano, ya yi aiki a matsayin Kwamishina na din-din-din a Hukumar Shari'a ta Jihar Kano.
Jogarancin jama'a
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Oktoban 2024, an naɗa Bashir a matsayin memba na kwamitin Shari'ah da aka sake nada na ƙungiyar Accounting and Auditing for Islamic Financial Institutions (AAOIFI) na wa'adin 2024-2028. Majalisar Koli ta Shari'ah a Najeriya (SCSN) ta sanar da nadinsa a matsayin sabon shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyatullah.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]|
|
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
|