Batilda Salha Burian
![]() | |||
---|---|---|---|
2005 - 2010 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 19 Oktoba 1965 (59 shekaru) | ||
ƙasa | Tanzaniya | ||
Harshen uwa | Harshen Swahili | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of London (en) ![]() | ||
Harsuna |
Turanci Harshen Swahili | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Batilda Salha Burian (an haife a ranar 19 ga watan Oktoba, 1965) 'yar siyasar ƙasar Tanzaniya ce kuma jakadiya.[1] Ita a halin yanzu; kwamishiniyar Yanki ce ta yankin Tanga.[1]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Burian ta sami digiri na uku a Kwalejin Jami'ar London a shekarar 1992. [2]
Ta yi wa'adi biyu a majalisar, daga shekarun 2000 zuwa 2005 sannan a shekarun 2006 zuwa 2010.[3] Tsakanin wa'adinta a majalisar, ta kasance mataimakiyar ministar ci gaban al'umma, jinsi da yara. Bayan Majalisar, ta zama Babbar Kwamishiniya (ko Jakadiyar Tanzaniya a Kenya).[4] A lokacin da take riƙe da muƙamin jakadiyar ƙasar Kenya, ta ci gaba da karfafa hulɗar dake tsakanin ƙasashen biyu, inda ta bayyana cewa, ƙasashen biyu suna da ma'ana sosai a fannin al'adu da muhalli.[5] A cikin shekarar 2015, ta zama jakadiyar Tanzaniya a Japan.[5]
Burian ta jagoranci taron sauyin yanayi na duniya III a shekarar 2009 a Geneva kuma ita ce wakiliyar dindindin na Tanzaniya a Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP).[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Mwangonde, Henry (6 February 2015). "Burian Moved to Japan from Kenya as Ambassador". The Citizen. Archived from the original on 13 July 2019. Retrieved 19 July 2015.
- ↑ "Hon. Dr. Batilda Salha Burian". Parliamentary Online Information System. The Parliament of Tanzania. Retrieved 19 July 2015.
- ↑ "Message from the High Commissioner Dr. Batilda Salha Burian". Tanzania: High Commission, Nairobi. Archived from the original on 20 July 2015. Retrieved 19 July 2015.
- ↑ "Message from the High Commissioner Dr. Batilda Salha Burian". Tanzania: High Commission, Nairobi. Archived from the original on 20 July 2015. Retrieved 19 July 2015.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 "Diplomacy of Development: 'Tanzania - Kenya Ties Built to Last'". Diplomat East Africa. 6 May 2014. Archived from the original on 21 July 2015. Retrieved 19 July 2015.