Jump to content

Beatrice Boateng

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Beatrice Boateng
Member of the 5th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2009 - 6 ga Janairu, 2013
District: New Juaben South Constituency (en) Fassara
Election: 2008 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Koforidua, 19 ga Augusta, 1951 (73 shekaru)
Karatu
Makaranta University of Edinburgh (mul) Fassara Master of Science (en) Fassara : karantarwa
Sana'a
Sana'a educational theorist (en) Fassara da ɗan siyasa
Imani
Addini Presbyterianism (en) Fassara
Jam'iyar siyasa New Patriotic Party

Beatrice Bernice Boateng 'yar siyasar Ghana ce kuma 'yar majalisa ta biyar 5 a jamhuriya ta 4 ta Ghana, a matsayin 'yar majalisa mai wakiltar mazabar Juaben ta Kudu a yankin Gabashin Ghana. [1]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Boateng a ranar 19 ga Agustan 1951 a Koforidua a Gabashin kasar Ghana . Ta halarci Jami'ar Edinburgh, Scotland a 2001 kuma tana da digiri na biyu a fannin ilimi. [2]

Ita ƙwararriyar ilimi ce kuma ta kasance Manajan Yanki na Makarantun Presbyterian a Babban yankin Accra . [1]

An fara zabe ta a matsayin ‘yar majalisa a kan tikitin jam’iyyar NPP a lokacin babban zaben watan Disamba na 2008 a matsayin ‘yar majalisa mai wakiltar mazabar New Juban ta Kudu . Beatrice ta samu kuri'u 34,409 wanda ke wakiltar kashi 61.3 cikin 100 na kuri'u 56,102 da aka kada.[1][3] Sai dai ta sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyarta a 2012 don haka ba za ta iya wakiltar jam'iyyar a zaben 2012 ba.[4]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Bazawara ce mai 'ya'ya uku. Ita 'yar Presbyterian ce. [1]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 nyame. "Ghana MPs – MP Details – Boateng, Bernice Beatrice (Ms)". www.ghanamps.com. Archived from the original on 3 April 2018. Retrieved 2 July 2020. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":02" defined multiple times with different content
  2. "Welcome to Ghana Members of Parliament Website". ghanamps.com. Archived from the original on 30 June 2020. Retrieved 2 July 2020.
  3. Ghana (2009). Ghana Gazette (in Turanci). Government Printer.
  4. "'I will not go Independent'-B.B. Boateng". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2 July 2020.