Jump to content

Bejan Daruwalla

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bejan Daruwalla
Rayuwa
Haihuwa Mumbai, 11 ga Yuli, 1931
ƙasa Indiya
British Raj (en) Fassara
Dominion of India (en) Fassara
Mutuwa Ahmedabad, 29 Mayu 2020
Sana'a
Sana'a astrologer (en) Fassara
Imani
Addini Hinduism (en) Fassara

Bejan Jehanjir Daruwalla[1] (11 Yuli 1931 – 29 Mayu 2020) masanin taurari ne kuma farfesa a harshen Ingilishi daga Indiya. Daruwalla ya kasance mai bauta ga Ganesha kuma yana amfani da hanyoyi daban-daban na hasashen taurari.

Tsohon farfesan harshen Ingilishi na asalin Parsi, Daruwalla ya kasance mai bauta ga Ganesha.[2][3][4]

Bejan Daruwalla ya rasu a ranar 29 ga Mayu 2020 a Ahmedabad, Indiya.[5] Rahotannin kafafen yada labarai sun nuna cewa ya mutu sakamakon cutar COVID-19. Amma, dansa Nastur, ya shaida wa The Times of India cewa mahaifinsa yana fama da cutar huhu da rashin iskar oxygen.[6]

Aikin Hasashen Taurari

[gyara sashe | gyara masomin]

Daruwalla ya yi amfani da hanyoyi kamar Numerology, Astrologiyar Hindu, Hannun Taurari, I Ching, Karatu da Tarot, Kabbalah da Astrologiyar Yamma.[3]

Ya bayyana hanyarsa ta yin hasashen da kalmomi kamar haka: "Da farko, idan mutumin yana nan, sai na duba shi na ji wani irin motsi. Na biyu, lokaci da ya zo yana da muhimmanci. Na uku, irin ranar da take, mai kyau, mara kyau ko matsakaici? Na hudu, layin tafin hannunsa. Na biyar, horoscope ɗin Indiya da kuma horoscope na yamma. Daga nan sai na dubi Ganesha kuma na yi hasashe."[2]

Kyaututtuka

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Game da Bejan Daruwalla". Astrologer Bejan Daruwalla (in Turanci). 30 Maris 2020. Check date values in: |date= (help)
  2. 2.0 2.1 "rediff.com: The Rediff Interview/Astrologer Bejan Daruwalla".
  3. 3.0 3.1 "Renowned astrologer Bejan Daruwalla passes away at 89; Guj CM tweets condolences". The Economic Times. 2020-05-29. Retrieved 2020-05-29.
  4. "World's Foremost Astrologer Bejan Daruwalla". Parsi Times. 30 Mayu 2020. Retrieved 5 Yuni 2020. Check date values in: |access-date= and |date= (help)
  5. "Bejan Daruwalla Renowned astrologer passes away at 88 | INDIA". EMEA Tribune (in Turanci). 2020-05-29. Retrieved 2020-05-29.
  6. "Noted astrologer Bejan Daruwalla loses battle to coronavirus at 88 in Ahmedabad".
  7. "World famous Astrologer Bejan Daruwalla gets lifetime achievement award - Tv9 Gujarati - video dailymotion". Dailymotion (in Turanci). 12 Janairu 2015. Check date values in: |date= (help)
  8. "Eminence Award 2019". www.bejandaruwalla.com (in Turanci).
  9. "Ganesha Bejan Daruwalla - Award Winning Celebrity Astrologer".

Hanyoyin Waje

[gyara sashe | gyara masomin]