Jump to content

Ben Stewart

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

 

Benjamin Richard Stewart ɗan siyasan Kanada ne, wanda ya jagoranci Kelowna ta yamma a Majalisar Dokokin Britaniya kolambiya daga 2018 har zuwa 2024 a matsayin memba na BC United (tsohon BC Liberal Party). A baya ya jagoranci yammacin-Kelowna daga 2009 zuwa 2013.

An fara zabarsa a zaben lardin na 2009. A cikin majalisa ta 39, a matsayin memba na Gwamnatin lardin ya yi aiki a matsayin Ministan Ayyukan 'Yan ƙasa a watan (Yuni 2009-Yuni 2010),saikuma Ministan Al'umma da cigaban Karkara (Yuni 2010-Oktoba 2010), da Ministan Aikin Gona (Oktoba 2010-Maris 2011). A ranar 5 ga Satumba, 2012, an sake nada shi a matsayin Ministan Ayyukan Jama'a dakuma budaddaiyar gwamnati.