Jump to content

Benjamin Uwajumogu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Benjamin Uwajumogu
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2019 - 18 Disamba 2019
District: Imo North
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 - ga Yuni, 2019
District: Imo North
Rayuwa
Haihuwa Okigwe, 30 ga Yuni, 1968
ƙasa Najeriya
Mutuwa Abuja, 18 Disamba 2019
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Benjamin Uwajumogu i (Yuni 30, 1968 - Disamba 18, 2019) [1] ɗan siyasan ne a Najeriya. [2] Ya kasance memba na jam'iyyar All Progressives Congress Party [A.P.C] wanda ke wakiltar gundumar Sanata ta Imo ta Arewa a jamhuriya ta 9 ta Majalisar Dokokin Najeriya kafin mutuwarsa.[3][4]

Rayuwa ta farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Uwajumogu a Okigwe, Ihitte Uboma, Jihar Imo, Najeriya a ranar 30 ga Yunin shekara ta 1968. [5]

Rayuwar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Maris na shekara ta 2018, Uwajumogu ya gabatar da wata shawara ga Majalisar Dattijai don hana aikin yara kuma ya bukaci Zartarwa da hukumomin ta da su tabbatar da aiwatar da Dokar 'Yancin Yara. [6]

A watan Yunin shekarar 2018, Uwajumogu ya yi murabus daga nadin sa a matsayin sakataren kwamitin taron kasa na APC kuma ya bayyana cewa saboda " dalilai na kansa ne".[7]

A ranar 26 ga watan Yulin shekara ta 2019, an rantsar da Uwajumogu a karo na biyu a matsayin Sanata wanda ke wakiltar Imo North. [8]

Mutuwa da sakamakonsa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ya koma Abuja daga Hadaddiyar Daular Larabawa don kula da rashin lafiyarsa na dogon lokaci, [9] Uwajumogu ya mutu a gidansa a ranar 18 ga Disamba, 2019, a Abuja. [10][11]

An gudanar da zaɓe a shekarar 2021 don cika kujerar Uwajumogu a majalisar dattijai inda Chukwuma Frank Ibezim ya gaje shi.[12]

Kyaututtuka da girmamawa

[gyara sashe | gyara masomin]
  • NUJ mutumin shekara, 2007.[13]
  1. Ogundipe, Samuel (2019-12-18). "BREAKING: Nigerian Senator Ben Uwajumogu is dead" (in Turanci). Retrieved 2019-12-18.
  2. "Even during, after the civil war no group had ever given Igbo ouit notice – Uwajumogu". Vanguard News (in Turanci). 2017-06-22. Retrieved 2019-04-14.
  3. "Senate: Full list of APC caucus who signed Ndume's removal". The Nation Nigeria (in Turanci). 2017-01-12. Retrieved 2019-04-14.
  4. "Senate halts, probes sale of Port Harcourt Refinery". guardian.ng. 31 May 2017. Retrieved 2019-04-14.
  5. Odunsi, Wale (2019-12-18). "Nigerian Senator is dead". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-10-20.
  6. Busari, Kemi (2018-03-06). "Nigerian Senate moves to curb child labour, enforce Child Rights Act". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-10-20.
  7. "Imo senator resigns as APC convention secretary -- to calm 'fraying nerves'". TheCable (in Turanci). 2018-06-02. Retrieved 2022-10-20.
  8. vanguard (2019-07-26). "Benjamin Uwajumogu Sworn in as Imo North Senator". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2022-10-20.
  9. Ogundipe, Samuel (2019-12-18). "Nigerian Senator Ben Uwajumogu is dead". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-10-24.
  10. Ogundipe, Samuel (2019-12-18). "BREAKING: Nigerian Senator Ben Uwajumogu is dead" (in Turanci). Retrieved 2019-12-18.
  11. Chidiebube, Okeoma (18 December 2019). "Imo Senator, Benjamin Uwajumogu, is dead". punchng.com.
  12. Jeremiah (2021-04-27). "BREAKING: Senate President Swears-in Ibezim As New Imo North Senator". Leadership News (in Turanci). Archived from the original on 2022-02-20. Retrieved 2022-02-20.
  13. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". www.nassnig.org. Archived from the original on 2020-10-09.