Betty Nambooze
![]() | |||
---|---|---|---|
![]() | |||
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa |
Mukono Town (en) ![]() | ||
ƙasa | Uganda | ||
Mazauni |
Mukono Town (en) ![]() | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar shahidan Uganda Law Development Centre (en) ![]() | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan jarida, ɗan siyasa da Lauya | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Democratic Party (en) ![]() |
Betty Nambooze Bakireke, wacce aka fi sani da Betty Nambooze, 'yar jarida ce kuma 'yar siyasa a ƙasar Uganda. Tana aiki a matsayin 'yar majalisa, mai wakiltar Mukono Municipality, a gundumar Mukono [1]
Tarihi da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haife ta a gundumar Mukono, ranar 13 ga watan Yuli, 1969. Ta halarci Makarantar Sakandare ta Bishop Mukono, ta kammala karatunta a shekarar 1986. [2] Daga baya ta halarci Cibiyar Ci gaban Shari'a, inda ta kammala karatun digiri a fannin shari'a, a shekarar 1998. A cikin shekarar 2010, Jami'ar Shuhada ta Uganda ta ba ta Difloma a cikin Nazarin Ci gaba. [1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]An fara zaɓen Nambooze a matsayin 'yar majalisa a watan Mayun 2010, lokacin da a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Democrat, ta doke ɗan majalisa mai ci a lokacin, Peter Bakaluba Mukasa na jam'iyyar National Resistance Movement mai mulki. [3] A cewar bayananta na majalisar, Nambooze ta yi aiki a matsayin mai ba da labarai (stringer), tsakanin shekarun 1993 zuwa 2000. Daga shekarun 2000 zuwa 2004, ta yi aiki a matsayin jami'in tilasta bin doka. Daga shekarun 2004 zuwa 2005, ta yi aiki a matsayin jami'in ma'aikata. Ta yi aiki a matsayin mai gabatar da rediyo tsakanin shekarun 2000 zuwa 2009 a CBS FM. Daga shekarun 2005 zuwa 2010, ta yi aiki a matsayin kakakin jam'iyyar Democratic Party a Uganda. [1][4]
A ranar 24 ga watan Fabrairun 2016, an kama ta a takaice tare da zaɓaɓɓen dan majalisar wakilai Moses Kasibante bisa bayyana wasu takardu da ke bayyana maguɗin zaɓe da aka yi a lokacin zaɓen ƙasar da aka yi kwanan nan.
An kama Nambooze a lokuta da dama bisa dalilai daban-daban na siyasa, galibi ana tuhumarta da karya, amma har yanzu ba a yanke mata hukunci ba a kowace kotu. [5] [6] [7] [8] Ita ma an yi mata barazana har ma da guba saboda ayyukanta na siyasa. [9] [10]
A ranar 13 ga watan Agusta, 2020, an ayyana Nambooze a matsayin memba na jam'iyyar siyasa ta "National Unity Platform" tare da dan uwanta ɗan majalisa "Kyagulanyi Sentamu Robert" aka "Bobi Wine" shugaban jam'iyyar. Tare da sauran 'yan jam'iyyarta, Nambooze sun shirya kan "Mission 2021" manufar jam'iyyar don sauke jam'iyya mai mulki a zaɓen shekara 2021 mai zuwa [11] [12]
A zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar na shekarar 2021, Namboze ta sake samun wa'adin mulki (2021-2026) don wakiltar ƙaramar hukumar mukono a kan tikitin jam'iyyar NUP bayan ta doke abokan takararta na kusa Mista George Fred Kagimu na Democratic Party (DP) da Abbas Ssozi na National resistance Movement (NRM). [13] [14] A ranar 19 ga watan Oktoba 'yan sanda sun gudanar da bincike kan harin da aka kai gidan Honourable Betty Nambooze inda suka gano sabbin pangas guda biyu a cikin buhu a cikin wani ƙaramin lambun tumatir [15] [16]
Ayyukan majalisa
[gyara sashe | gyara masomin]Nambooze ta zauna a (a) Kwamitin Ma'aikata da Ƙananan Hukumomi da (b) Kwamitin Kula da Asusun Ƙananan Hukumomi. [1] [17]
Na sirri
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Nuwamba 2002, Betty Nambooze ta auri Henry Bakireke, wanda ta haɗu da shi a makarantar sakandare a shekarun 1980. Tare, su ne iyayen yara sama da 6, na halitta da na riko. [2][18]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Majalisar Uganda
- Charles Ayume
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 POU (6 January 2016). "Profile of Mrs. Bakireke Nambooze Betty, Member of Parliament for Mukono County North, Mukono District". Parliament of Uganda (POU). Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 6 January 2016.
- ↑ 2.0 2.1 Kimbowa, Joseph (4 December 2012). "Nambooze, Bakireke love trek started in S.3". Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 7 January 2016.
- ↑ Edris Kiggundu, and Hussien Bogere (26 May 2010). "How Nambooze trounced NRM". Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 7 January 2016.
- ↑ Clarke, Jody. "How to keep winning elections - Ugandan style". The Irish Times (in Turanci). Retrieved 2021-04-03.
- ↑ Ifex Network (31 March 2017). "Police attack journalists covering arrest of Ugandan opposition MP". Ifex.org Quoting Human Rights Network for Journalists - Uganda. Retrieved 23 June 2018.
- ↑ Thembo, Johnson (23 April 2017). "Good vs Bad DP: MP Nambooze Arrested, Injured And Tortured in Masaka". The Insider (Uganda). Retrieved 23 June 2017.
- ↑ Sabano, Jessica (13 June 2018). "Abiriga murder: MP Nambooze arrested". Retrieved 23 June 2018.
- ↑ paseditor (2018-09-17). "The Leader of the Opposition, Betty Aol Ocan visits Hon Betty Namboze at her home in Mukono, August 31st 2018". www.parliament.go.ug (in Turanci). Retrieved 2021-04-03.
- ↑ Kaaya, Sadab Kitatta. "Nambooze: I was poisoned". The Observer - Uganda (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-10. Retrieved 2021-04-03.
- ↑ Malaba, Tom. "Police to Disperse Nambozes Rally". Uganda Radio Network (in Turanci). Retrieved 2021-04-03.
- ↑ "Good Thursday! Bobi Wine's budding NUP captures 11 DP MPs and singer Chameleon". PML Daily (in Turanci). 2020-08-13. Retrieved 2020-08-30.
- ↑ Writer, TRACY TEDDY NAYIGA | PML Daily Staff (2020-10-14). "MP Nambooze appeals to NUP losers to Support the Flag bearers". PML Daily (in Turanci). Retrieved 2021-04-03.
- ↑ "Who will succeed Betty Ocan as LoP?". Daily Monitor (in Turanci). 29 January 2021. Retrieved 2021-04-03.
- ↑ "NRM teams up with DP to beat Nambooze in Mukono". Daily Monitor (in Turanci). 12 January 2021. Retrieved 2021-04-03.
- ↑ "Police Probes Attack at MP Nambooze's Home - SoftPower News" (in Turanci). 2021-10-19. Retrieved 2021-11-16.
- ↑ spyreports. "Just In: MP Betty Nambooze Attacked At Her Home". Spyreports (in Turanci). Retrieved 2021-11-16.[permanent dead link]
- ↑ "So many questions, very few answers on the 43 new counties – Parliament Watch". parliamentwatch.ug. Retrieved 2021-04-03.
- ↑ The political Life of Hon.Betty Nambooze member of parliament mukono municipality | People and Power (in Turanci), retrieved 2021-04-03