Bikin al'ada na Rusinga

Bikin al'adun Rusinga bikin kwana biyu ne na shekara-shekara na al'adun mutanen Abasuba na Kenya.[1] ana yin shi a ranar Alhamis da Juma'a na ƙarshe kafin Kirsimeti a tsibirin Rusinga. Anne Eboso [2] ce ta kafa wannan biki kuma ta gudanar da ita ta Cibiyar Al'adu ta Chula.[3]
Bikin al'adun Rusinga shine bikin mafi girma na kiyaye al'adun Abasuba waɗanda galibi ana samun su a tsibirin Rusinga da tsibirin Mfangano a tafkin Victoria a yankin Kenya na tafkin. Al'adar Abasuba tana fuskantar matsin lamba daga al'ummar Luo da ke makwabtaka da ita saboda cudanya da auratayya.[[4]] [5] Harshen Suba Hukumar Kula da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta sanya shi a cikin Atlas of the World's Languages in Danger a matsayin daya daga cikin harsuna goma sha uku da ke cikin hadari a Kenya[6] aka kebe shi a matsayin mai rauni.
Bikin yana magance matsalolin al'umma a cikin al'ummar Abasuba kamar yadda ake yin jima'i da kifi da ke yin tasiri mara kyau ga kokarin dakile yaduwar cutar kanjamau.[7]
Kiɗa
[gyara sashe | gyara masomin]Bikin Al'adun Rusinga yana da wasan bvkwaikwayo na gargajiya da na zamani.[8]] annan wa] annan wa] annan wa] ansu kasance a cikin nau'in wasan kwaikwayo na }ungiyoyin al'adu da kuma kungiyoyin mawakan gargajiya na Abasuba. Ana yin waƙar gargajiya a cikin harshen Subanese. Abubuwan da suka fi daukar hankalin al'adu sun kasance a wuraren wasanni na bikin. Kafin gasar tseren kwale-kwale, ’yan wasan kwaikwayo da masu halartar biki sun tashi daga harabar bikin kuma su ƙaura zuwa ruwan tafkin Victoria, tare da kaɗe-kaɗe da raye-rayen gargajiya.
al adunsaa
[gyara sashe | gyara masomin]Al'adar Abasuba ita ce bikin farko na bikin al'adun Rusinga.[9] An baje kolin fuskoki daban-daban na al'adun Abasuba a wajen bikin. An baje kolin kayan tarihi na aikin yumbu, aikin katako da rayuwar Abasuba na yau da kullun da ke nuna al'adun Abasuba a wurin bikin. Kade-kade, abinci, wasannin motsa jiki da duk wani taron da ke faruwa a wurin bikin suna da manufar ingantawa da kiyaye al'adun Abasuba
Abinci
[gyara sashe | gyara masomin]Abinci a bikin al'adun Rusinga ya haɗa da kayan abinci na gargajiya da abinci na zamani. Wasu daga cikin abincin gargajiya da ake samu a wurin bikin suna ɗaukar lokaci mai tsawo don shirya kuma suna samuwa ne kawai na ɗan gajeren lokaci - yawanci ranar farko ta bikin. Abubuwan jin daɗi da ake samu sun haɗa da naman da aka shirya na gargajiya, kayan lambu da sauran jita-jita.
manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ The Star Newspaper Kenya. "The Rusinga Festival thrills". Star Newspaper website. The Star. Retrieved 10 January 2017.
- ↑ ]IREX, IREX. "IREX Website". IREX. International Research and Exchanges Board. Retrieved 10 January 2017.
- ↑ The Star Newspaper Kenya. "The Rusinga Festival thrills". Star Newspaper website. The Str. Retrieved 10 January 2017.
- ↑ The East African. "Extinction of languages in East Africa worries UNESCO". The East African Website. The East African. Retrieved 10 January 2017
- ↑ Endangered Languages Project. "Endangered Languages Project: Suba Language". Endangered Languages Project. Endangered Languages Project. Retrieved 10 January 2017.
- ↑ UNESCO. "Endangered Languages". UNESCO Languages Atlas. UNESCO. Retrieved 10 January 2017.
- ↑ Nation. "Homa Bay leads country in HIV/Aids cases, new study says". Daily Nation. Daily Nation. Retrieved 10 January 2017.
- ↑ Capital FM. "Cultural Festivals in Kenya". Capital FM Kenya Website. Capital FM Kenya. Retrieved 10 January 2017.
- ↑ "The Rusinga Festival thrills"