Jump to content

Binta Kofar Soro

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Binta Kofar Soro
Rayuwa
Haihuwa 1970
Mutuwa 2019
Sana'a

Hajiya Binta Kofar Soro ko Hajiya Binta a takaice, kamar yanda abokan sana’arta na masana'antar Kannywood ke yawan kiranta. (An haife ta a ranar 24 ga watan Nuwamba na shekara ta alif dari tara da saba'in 1970, ta rasu a ranar 4 ga watan mayu shekara ta alif dubu biyu da sha Tara 2019), a cikin kwaryar birnin Katsina. Ta kasance Fitacciyar Jaruma ce a masana’antar kannywood.

Farkon Rayuwa da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi karatunta na addini da na zamani duk a garin Katsina kamin ta yi aurenta na farko.

Fitacciyar jarumar tana yawan fitowa a matsayin uwa a shurye shiryen shirin Kannywood matsayin da ya wuce gaban wasan kwaikwayo, har a zahiri yan wasan suna ɗaukarta tamkar uwa a garesu saboda rikon gaskiya, tausayi, shawarar da take basu kamar ita ta haifesu. Hajiya yar siyasace ta sahun gaba wadda take gwagwarmayar kwato ma tallakawan yankinta yancinsu da ake danne masu, yar kasuwace ita, sannan sai sana’ar da munka santa da ita wato wasan kwaikwayo wadda a cikinta ta yi fice wanda shike. Tana daukar matsayin uwa a faifayen shirin da take fitowa kamar irinsu Hajara Usman, wani lokacin ta fito matsayi irin na su Saratu Daso wato Muguwa ko Mayya.

Hajiya Binta tana daga cikin 'yan wasan kwaikwayo yan asalin Jahar Katsina da ke haskaka akwatunan kallon masu kallo.

GobirMob na taya daukacin Masana’antar Kannywood da Katsina jimamin mutuwar Hajiya Binta Kofa Soro.[1]

Hajiya Binta kofar soro Allah yayi mata rasuwa ranar asabar, wacce tayi daidai da 4 ga watan mayu shekara ta 2019, a gidanta da ke unguwar Fillin Samji dake cikin kwaryar birnin katsina.[2]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-01-28. Retrieved 2020-11-12.
  2. https://www.bbc.com/hausa/labarai-48170411