Jump to content

Birnin Kebbi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Birnin Kebbi

Wuri
Map
 12°27′N 4°12′E / 12.45°N 4.2°E / 12.45; 4.2
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Kebbi
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi125,594
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara228 m
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwasupervisory councillors of Birnin Kebbi local government (en) Fassara
Gangar majalisaBirnin Kebbi legislative council (en) Fassara

Birnin Kebbi, birni ne wanda yake a yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya. Shine cibiyar Jahar Kebbi kuma shine mazaunin Masarautar Gwandu. A kidayar shekara ta 2007 akwai yawan jama'a a birnin kimanin 125,594. Kebbi mafiya yawan mutanen jahar Hausawa ne da Fulani kuma Musulunci ne addinin da kuma yafi rinjaya a birnin. Birnin Kebbi ne mazaunin fadar Masarautar Kebbi a da, wadda daga baya ta koma garin Argungu bayan bude ta da Gwandu ya yi a shekara ta 1831.[1]

Taswirar kogin Sokoto

Birnin Kebbi na nan gefen kogin Sokoto wato Sokoto River. Akwai hanyar da ta hada birnin da garin Argungu (kilomita 45 daga Arewamaso gabashin birnin), Jega (kilomita 35 kudu maso gabas), da Bunza (kilimita 45 Kudu maso Yamma). [2]

  1. https://www.britannica.com/place/Birnin-Kebbi
  2. https://theconversation.com/institutions/federal-university-birnin-kebbi-2878