Jump to content

Bitrus Anosike

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bitrus Anosike
Rayuwa
HaihuwaLagos, 24 Disamba 1976 (49 shekaru)
ƙasaNajeriya
Sana'a
Sana'aɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
KAA Gent (en) Fassara-
Perth Glory FC (en) Fassara-
Bridge FC-
Hougang United FC (en) Fassara-
K.M.S.K. Deinze (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewaAtaka
Tsayi169 cm

Peter Ikechukwu Anosike Listen ⓘ (an haife shi a ranar 24 ga Disamba 1976) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya wanda ya taka leda a matsayin ɗan wasan gaba .

Aikin kulob

[gyara sashe | gyara masomin]

Anosike ya fara aikinsa ne da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Belgium mai suna AA Gent, inda ya buga wasanni biyu a gasar ba tare da ya zura ƙwallo ba. A ranar 21 ga Oktoba 1995, ya fara bugawa ƙungiyar AA Gent wasa a lokacin da suka sha kashi a hannun Anderlecht da ci 3-0. [1] A shekarar 1996, ya sanya hannu kan yarjejeniyar komawa ƙungiyar Deinze a matakin rukuni na biyu na ƙasar Belgium. [2]

A shekarar 1997, Anosike ya sanya hannu a kulob din Perth Glory na kasar Australia, inda ya ci kwallo a wasan farko da West Adelaide . [3] Kafin kakar wasa ta 1999, Anosike ya sanya hannu a kungiyar Hougang United da ke Singapore. [4]

Aikin ƙasa da ƙasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Anosike ya wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 'yan kasa da shekara 17 ta shekarar 1993, inda ya taimaka musu su lashe gasar sannan ya zura kwallon da ta ba su nasara a wasan karshe da Ghana . [1]

  1. ↑ Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named "net".
  2. ↑ "BEERSCHOT". lesoir.be. August 1996.
  3. ↑ "1997/1998 Season Round 08 Results". ozfootball.net (Archived). Archived from the original on 11 February 2015.
  4. ↑ "Singapore 1999". RSSSF.