Jump to content

BlueforSudan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
BlueforSudan
# (mul) Fassara da Internet activism (en) Fassara
Bayanai
Farawa ga Yuni, 2019
Ƙasa Sudan
Muhimmin darasi Khartoum massacre
Hashtag (mul) Fassara BlueforSudan da BlueForSudan

A watan Disamba na shekarar 2018, zanga-zangar ta tashi a Sudan, wanda ya Haifar da rikice-rikice da ruguzewar tattalin arzikin kasar. An fara zanga-zangar ne a garin Atbara, wanda ke arewa maso gabashin kasar, kuma da sauri zanga-zaganar ta bazu a duk faɗin kasar.[1] Mutanen Sudan a Wanan Lokacin sunyi fama da hauhawar farashi, hauhawar farashin kayayyaki masarufi da na amfani, da kuma karancin tsabar kudi. Mutane da yawa sun zargi gwamnati da alhakin ruguzewar tattalin arziki, wanda suka yi imanin cewa cin hanci da rashawa ne ya haifar da shi.[2]

zanga-zangar bawai kawai game da ruguzewar tattalin arziki ba ne. Shugaban Sudan na dogon lokaci, Omar al-Bashir, ya kasance a mulki tun 1989 bayan juyin mulkin soja, kuma an san mulkinsa akwai dabaru na zalunci a kan 'yan adawa da kuma kungiyoyin farar hula. An zargi gwamnatin Al-Bashir da cin zarafin 'yancin ɗan adam, gami da azabtarwa, kisan kai ba tare da shari'a ba, da ƙuntatawa kan' yancin faɗar albarkacin baki da na manema labarai. Saboda haka, zanga-zangar ta faro ne a Kan haka da kuma niyyar kawar da mulkin kama Karya a kasar .[3]

Amsar da gwamnati ta bayar game da zanga-zangar ta kasance mai tsauri ce . Sojojin tsaro sun yi amfani da (tear gas) borkonon tsohowa, harsashi mai rai, da sauran nau'ikan tashin hankali don watsar da masu zanga-zangar. Har zuwa yau, gwamnatin ta sanya dokar hana fita kuma ta kuma rufe yanar Gizo don hana yaduwar labarai game da zanga-zangar. Kuma, zanga-zangar ta ci gaba da yaduwa,tare da samu ƙarin mutane da yawa da suka shiga.[1]

zanga-zangar ta kuma haifar da rikice-rikicen siyasa a Kasar Sudan, tare da neman korar al-Bashir da ke kara karfi a lokacin. A watan Afrilu na shekarar 2019, bayan anyi watanni anayin zanga-zangar, daga Karshe sojojin sunyi nasarar koran al-Bashir kuma sun mallaki gwamnati ta hanyar juyin mulki. Kuma, yawancin mutanen Sudan, waɗanda suka ci gaba da neman mulkin farar hula, ba su yi maraba da mulkin soja ba. Wannan ne ya haifar da rikici tsakanin sojoji da kuma masu zanga-zangar, tare da tattaunawa don tantance yanda makomar siyasar Zata kasance a kasar .[3]

Zama da akayi da Jama'a a hedikwatar sojoji na Khartoum sun taka muhimmiyar rawa a juyin juya halin Sudan.Gurin zaman ya kasance a cikin Khartoum, wanda zaman ya farane a ranar 6 ga watan Afrilu [4] kusa da hedikwatar sojojin kasa,sojojin ruwa,da kuma rundunar sojojin sama. Ya zama alama ce ta yunkurin juya mulkin farar hula a kasar Sudan.[5] Wurin ya kasance inda masu zanga-zangar za su iya taruwa don neman canjin siyasa da kuma kira ga a cire shugaban Kasar Sudan na dogon lokaci,Omar al-Bashir, wanda ke mulki tun bayan juyin mulkin soja a shekarar 1989.[6]

Shafin ya kasance a cikin zaman lafiya kuma ya zama cibiyar aiki, tare da masu zanga-zangar da ke kafa mataki don jawabai da kiɗa, da Samar da guri don mutane su yi barci a ciki.[5] Wuri ne inda mutanen Sudan suka hadu daga yankuna daban-daban, yaroroka daban-daban, masu addinai daban-daban suka taru don nuna takaicin su ga cin hanci da rashawa da kuma yanayin tattalin arziki mara kyau.[6] A lokacin akwai daliba mai suna, Alaa Salah, me shekaru 22 a Sudan a fannin injiniyanci da gine-gine a Khartoum, ta zama a gaba wajen zanga-zangar a Sudan lokacin da hotona na jagoranta a lokacin zaman ya bazu a watan Afrilu na shekara ta 2019.

Kafin Kisan kiyashi na 3 ga Yuni, gwamnati ta yi ƙoƙari ta murkushe zanga-zangar tare da matakai daban-daban. Wadannan sun hada da ayyana dokar ta baci, rufe intanet, da kuma amfani da cakuda karfi da tattaunawa don kokarin shawo kan masu zanga-zangar su warwatse.[7] Koyaya, masu zanga-zangar sun ci gaba, kuma zaman da aka yi a hedikwatar soja a Khartoum ya karu da girma da mahimmanci, daga ƙarshe ya zama cibiyar juyin juya halin a Sudan.[6]

Gwamnatin Sudan ta mayar da martani ga zanga-zangar da karin tashin hankali. Gwamnati ta yi amfani da iskar hawaye, harsashi mai rai, da duka don watsar da masu zanga-zangar.[5] Bugu da kari, Sojojin Taimako da Saurin sun kai hari wurin zama a ranar 3 ga Yuni 2019, inda suka kashe 112 kuma suka jikkata masu zanga-zangar sama da 700 kuma suka lalata yanayin zaman lafiya na zaman.[5][8]

  1. 1.0 1.1 "12 defining moments in Sudan's 12-month uprising". AlJazeera (in Turanci). 2019-12-18. Archived from the original on 2022-10-21. Retrieved 2023-04-01. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":2" defined multiple times with different content
  2. Copnall, James (2019-07-07). "Sudan's Third Revolution". History Today. Archived from the original on 2022-12-04. Retrieved 2023-04-01.
  3. 3.0 3.1 Searcy, Kim (June 2019). "Sudan in Crisis". Origins (in Turanci). Archived from the original on 2022-05-27. Retrieved 2023-04-01. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":3" defined multiple times with different content
  4. Abazer, Rawan (2019-05-05). "Inside Al Qeyada". 500 Words Magazine (in Turanci). Archived from the original on 2022-05-03. Retrieved 2023-04-01.
  5. 5.0 5.1 5.2 5.3 Fricke, Adrienne (2020-03-05). "'Chaos and Fire': An Analysis of Sudan's 3 June 2019 Khartoum Massacre". PHR (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-01. Retrieved 2023-04-01. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":4" defined multiple times with different content
  6. 6.0 6.1 6.2 El Amin, Rahba (2019-07-03). "Al Qeyada: A New World Inside of a Country". 500 Words Magazine (in Turanci). Archived from the original on 2023-04-01. Retrieved 2023-04-01. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":5" defined multiple times with different content
  7. Bahreldin, Ibrahim Z. (January 2020). "Beyond the Sit-In: Public Space Production and Appropriation in Sudan's December Revolution, 2018". Sustainability (in Turanci). 12 (12): 5194. Bibcode:2020Sust...12.5194B. doi:10.3390/su12125194. ISSN 2071-1050.
  8. Lichtenstein, Amanda; Baerendtsen, Pernille (2019-06-16). "Global Voices - Social media goes blue for Sudan". Global Voices (in Turanci). Archived from the original on 2022-12-25. Retrieved 2023-04-01.