Bob Nwannunu
Appearance
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2003 - Chris Adighije → District: Abia Central | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Jihar Abiya, 20 century | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||
| Mutuwa | 30 Mayu 2003 | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | All People's Party | ||
John Bob Nwannnunu Ɗan siyasar Najeriya ne. An zaɓe shi Sanata mai wakiltar mazabar Abia ta tsakiya a jihar Abia a Najeriya a farkon jamhuriya ta hudu ta Najeriya, inda ya tsaya takara a jam'iyyar All People's Party (APP). Ya fara aiki a ranar 29 ga Mayu 1999.[1]
Bayan ya hau kujerarsa a Majalisar Dattawa an nada shi kwamitocin Zabe, Man Fetur, Sadarwa, Wutar Lantarki da Karfe da Noma.[2] Shi ne mataimakin shugaban APP a majalisar dattawa.[3] A cikin watan Janairun 2001, yayin da yake magana kan shirin tsige majalisar ministocin da shugaba Olusegun Obasanjo ya yi, ya ce tawagar ministocin Obasanjo na farko sun gaza yin aiki a ofis saboda sun zuba ido kan harkokin siyasa na gaba.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "FEDERAL REPUBLIC OF NIGERIA LEGISLATIVE ELECTION OF 20 FEBRUARY AND 7 MARCH 1999". Psephos. Retrieved 2010-06-19
- ↑ "Congressional Committees". Nigeria Congress. Archived from the original on 2009-11-18. Retrieved 2010-06-19.
- ↑ Chukwudi Nwabuko (2001-04-29). "Haruna Abubakar: Toxic Fuel as Archile's Heel". ThisDay. Archived from the original on 2005-11-20. Retrieved 2010-06-19
- ↑ Chukwudi Nwabuko Chuks Okocha, Goddy Eweremadu and Tokunbo Adedoja (2001-01-30). "Cabinet: President Briefs Na'Abba, Mantu, Others". ThisDay. Archived from the original on 2004-12-10. Retrieved 2010-06-19.