Burj Khalifa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Burj Khalifa.

Burj Khalifa (larabci برخ خليفة ) wani gini ne wai tsawon gaske dake a kasar Daular Larabawa wato Dubai. Shine gini mafi tsawo a Duniya baki daya tun daga shekara 2008 da tsawon murabbain mita 829.8 (kafa 2722)

An fara ginin ne tun daga shekara 2004 kuma an bude ginin ne a shekarar 2010 a wani bangare na sabon cigaba. Gwamnatin kasar ce ta dauki nauyin ginin daga kudin da take samu na rarar man fetur a kasar. Da farko an sakama ginin sunan Burj Dubai ne amma dag baya aka sauya masa suna zuwa Burj Khalifa domin girmama jagoran birnin Abu Dhabi kuma shugaban kasar Khalifa Bin Zayed Al Nahyan. Ginin ya rusa kowanne tarihi na hini mafi tsayi a duniya.

Yadda tsarin ginin ya kasance[gyara sashe | Gyara masomin]

Zanen yadda akaita canza fasalin ginin.
Kamfanin TeiPei ne ya kaddamar da ginin da zanen taswirar sa.

Ginin yai kamanceceniya da ginin Willis Tower dake kasar Amurika dakuma ginin masallacin Samarra.

Ginin masallacin Samarra.