Caleb Zagi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Caleb Zagi
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
District: Kaduna South
Rayuwa
Haihuwa Jihar Kaduna, Oktoba 1960 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Caleb Zagi (an haife shi a watan Oktoba shekarar 1960) an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu a jihar Kaduna, Najeriya, ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayu shekarar 2007. Ya kasance ɗan jam'iyyar (PDP).[1]

Zagi ya sami digiri na biyu a fannin kasuwanci. An zaɓe shi a Majalisar Wakilai a shekarar 2003, yana riƙe da mukamin har zuwa shekarar 2007. Ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP a matsayin ɗan takarar sanata a shiyyar kudancin Kaduna, amma a watan Janairun 2007 ya fuskanci matsananciyar matsin lamba kan ya miƙa tikitin takararsa ga Sanata mai ci Isaiah Balat, sai dai yaƙi amincewa da hakan, an bashi tayin ya tsaya takara a kan tikitin mataimakin gwamna na jam’iyyar. Zagi ya ki ba da tikitin, a ƙarshe kuma aka zaɓe shi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kaduna PDP". Newswatch. January 22, 2007. Archived from the original on 2012-03-12. Retrieved 17 October 2022.