Candice Mwakalyelye
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | 8 ga Augusta, 1986 (39 shekaru) |
| Sana'a | |
| Sana'a | mai gabatarwa a talabijin |
Candace Mwakalyelye mai watsa shirye-shiryen TV ce da rediyo kuma mai aikin watsa labarai.
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mwakalyelye a ranar 8 ga watan Agusta 1986. Ba a san da yawa game da mahaifarta da mahaifanta ba ko da yake wasu majiyoyi sun ce rabin 'yan Tanzaniya ne rabin kuma 'yan Zimbabwe ne. [1]
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Mwakalyelye, wacce laƙabinta shine NdiCandice ko Malkia, Sarauniyar Lion, mai watsa shirye-shiryen TV ce da rediyo, ma'aikacin'yar watsa labarai, MC kuma jakadiyar alama wacce a halin yanzu ke zaune a Zimbabwe. [2] Ta yi aiki a Tanzaniya na watsa shirye-shirye a can da kuma a kamfanoni masu zaman kansu.
Ta yi aiki da ZiFM daga shekarun 2012, gidan rediyo a Zimbabwe kuma ta bari a shekarar 2016 kafin ta dawo a shekarar 2018. [3] Ita ce ta lashe kyaututtuka daban-daban da suka haɗa da Megafest National Business Awards-Media and Business Information Personality of the Year (2013), Zimbabuwe International Women Awards- Media Professional of the Year (2015).
A matsayinta na MC, ta karɓi bakuncin babbar lambar yabo ta Zimbabwe Achievers wanda aka gudanar a Landan. [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Activists campaign to end discrimination against albinos in Zimbabwe". VOA (in Turanci). Retrieved 2021-12-04.
- ↑ "Interview With Radio Personality Candice Mwakalyelye". Youth Village Zimbabwe (in Turanci). 2015-07-29. Retrieved 2021-12-04.
- ↑ Chronicle, The. "Candice rejoins ZiFM Stereo". The Chronicle (in Turanci). Retrieved 2021-12-04.
- ↑ "Radio Personality Candice Mwakalyelye To Host Zim Achievers Gala". 263Chat (in Turanci). 2017-05-04. Archived from the original on 2021-12-03. Retrieved 2021-12-04.