Jump to content

Cape Malays

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Cape Malays (a cikin Afrikaans: Kaapse Maleiers, da kuma کاپز ملیس a haruffan Larabci), waɗanda ake kuma kira Cape Muslims ko Malays, wata al’umma ce ta Musulmai ko kuma ƙabila a Afirka ta Kudu. Su ne zuriyar bayi da kuma ’yantattu Musulmai daga sassa daban-daban na duniya, musamman daga Indonesia (wanda a wancan lokacin ake kira Dutch East Indies) da wasu ƙasashen Asiya, waɗanda suka zauna a Cape a lokacin mulkin Holland da Birtaniya.[1][2] Ko da yake farkon mambobin wannan al’umma sun fito ne daga ƙasashen mallakar Holland na kudu maso gabashin Asiya, zuwa shekarun 1800 an fara amfani da kalmar “Malay” don kiran dukkan Musulman da ke Cape, ba tare da la’akari da asali ba. Tunda suna amfani da yaren Malay a matsayin yaren sadarwa da kuma koyar da addini, sai al’ummar ta zama sananniya da sunan “Malays.” Yawancin Malays suna zaune ne a yankin Cape Town. Wannan al’umma ta taka muhimmiyar rawa a tarihin addinin Musulunci a Afirka ta Kudu, kuma al’adunsu na girke-girke sun zama wani muhimmin ɓangare na abincin gargajiya na ƙasar. Malays sun taimaka wajen haɓaka harshen Afrikaans a rubuce, inda a farko suka riƙa amfani da haruffan Larabci. A zamanin mulkin wariyar launin fata (apartheid), an ware kalmar “Malay” a matsayin wani rukuni ƙarƙashin ƙungiyar masu launin fata (Coloured) ta doka.

Karin bayani: Islam a Afirka ta Kudu § Lokacin VOC Kamfanin Dutch East India (VOC) ya kafa wata mallaka a Cape of Good Hope (wanda ake kira Dutch Cape Colony) a matsayin wuri na sauka da cika kaya ga jiragen ruwa masu tafiya tsakanin Turai da Asiya, wanda daga baya ya zama birnin Cape Town. Har ila yau, Hollandawa sun mamaye Dutch East Indies (wanda a yau ake kira Indonesia),[3] wanda ya kasance wani ɓangare na daular Holland na tsawon ƙarni da dama, da kuma Dutch Malacca, wanda suka riƙe daga 1641 har zuwa 1824.[4] Shuwagabannin Musulunci irin su Sheikh Yusuf, wani hamshakin ɗan mulkin Makassar kuma malami daga Sulawesi, wanda ya yi wa kamfanin turawan mulkin mallaka (VOC) tawaye a yankin kudu maso gabashin Asiya, an yi masa kora zuwa Afirka ta Kudu. [5]Bayan sa kuma, bayi daga wasu sassan Asiya da Afirka suka biyo. Ko da yake ba a iya sanin ainihin asalin bayi da aka kawo Cape da cikakken tabbas ba, an kiyasta cewa kaso madaidaici ne aka kawo daga Malagasi, Indiyawa, Insulindiyawa (mutanen kudu maso gabashin Asiya), da kuma Afirikawa na nahiyar.[6] Wasu rahotanni sun nuna cewa mafi yawan bayi sun fito ne daga Madagascar. Yawan 'yan siyasar Musulmi da aka kira “Indiaanen” da “Mohammedaanen” daga kudu maso gabashin Asiya an tsare su a tsibirin Robben Island. Daga cikin su akwai Tuan Guru, babban limamin farko a Afirka ta Kudu. Sheikh Madura ma an kora shi a cikin shekarun 1740s kuma ya rasu a Robben Island; har yanzu maƙabar sa (kramat) na nan.[7]

  1. Stell, Gerald (2007). "From Kitaab-Hollandsch to Kitaab-Afrikaans: The evolution of a non-white literary variety at the Cape (1856-1940)". Stellenbosch Papers in Linguistics (PDF). Stellenbosch University. 37. doi:10.5774/37-0-16.
  2. "The Indonesian anti-colonial roots of Islam in South Africa". 25 August 2016. Retrieved 11 April 2022.
  3. Vahed, Goolam (13 April 2016). "The Cape Malay:The Quest for 'Malay' Identity in Apartheid South Africa". South African History Online. Retrieved 29 November 2016.
  4. Wan Hashim Wan Teh (24 November 2009). "Melayu Minoriti dan Diaspora; Penghijrahan dan Jati Diri" [Malay Minorities and Diaspora; Migration and Self Identity] (in Harshen Malay). Malay Civilization Seminar 1. Archived from the original on 22 July 2011.
  5. Winstedt, Sir Richard Olof (1951). "Ch. VI: The Dutch at Malacca". Malaya and Its History. London: Hutchinson University Library. p. 47.
  6. Stell, Gerald; Luffin, Xavier; Rakiep, Muttaqin (2008). "Religious and secular Cape Malay Afrikaans: Literary varieties used by Shaykh Hanif Edwards (1906-1958)". Bijdragen tot de Taal-, Land- en Volkenkunde / Journal of the Humanities and Social Sciences of Southeast Asia. 163 (2–3): 289–325. doi:10.1163/22134379-90003687. ISSN 0006-2294.
  7. Davis, Rebecca. "Bo-Kaap's complicated history and its many myths". ewn.co.za.