Caroline Kamusiime
|
| |||
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Uganda, 23 Nuwamba, 1982 (43 shekaru) | ||
| ƙasa | Uganda | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
Makarantar Sakandare ta Kololo Jami'ar Makerere | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a |
legislator (en) | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa |
National Resistance Movement (en) | ||
Caroline Kamusiime (an Haife ta a ranar 23 ga watan Nuwamba 1982) 'yar majalisar dokoki ce 'yar Yuganda wacce ke wakiltar mutanen gundumar Rukiga a matsayin mace 'yar majalisar dokokin Uganda.[1][2][3] Ita mamba ce ta jam'iyyar National Resistance Movement (NRM) [4] jam'iyyar a shugabancin siyasa a Uganda ƙarƙashin jagorancin Yoweri Kaguta Museveni shugaban jamhuriyar Uganda. [5]
Kamusiime ta kasance wata ɓangare na kokarin gano bakin zaren warware takaddama da sanyin alakar da ke tsakanin Ruwanda da Uganda,[6][7][8] inda Ruwanda ta rufe iyakokinta da Uganda tana zargin Uganda da bayar da kuɗaɗe ga wasu da ke son ruguza gwamnatin Rwanda.
A shekarar 2021, an sake zaɓen ta a matsayin 'yar majalisa. [9] [10]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Kamusiime ta yi karatunta na O'level daga makarantar sakandare ta kololo inda ta zauna zana takardar shaidar ilimi ta Uganda (UCE) a shekarar 1997. Daga baya ta shiga bishop comboni college kanungu inda ta kamala samun takardar shedar ilimi ta Uganda (UACE) a shekarar 1999. Daga baya ta sami digiri na farko a fannin fasahar sadarwa daga jami'ar Makerere a shekarar 2010. [11]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Kamusiime ta kasance 'yar majalisar dokokin Uganda daga shekarar 2017 zuwa yau. [11] [12]
Ta kasance jami'ar fasahar sadarwa a MTN Uganda daga shekarun 2011 zuwa 2016, [11]
Ta kuma kasance jami'in tebur na gaba a kamfanin taɓa na Burtaniya da Amurka Uganda daga shekarun 2006 zuwa 2010 [11] kuma ta kasance mai lissafin kuɗi na caltex Uganda daga shekarun 2000 zuwa 2006 [11]
A cikin majalisar dokokin Uganda, tana aiki a kwamitin shari'a da na majalisa. [13]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Job Namanya (2017-08-23). "Rukiga elects NRM flag bearers".
- ↑ "Woman member of parliament rukiga district". ELECTORAL COMMISSION. Retrieved 2020-04-17.
- ↑ "Woman member of parliament rukiga district". ELECTORAL COMMISSION. Retrieved 2020-04-17.
- ↑ Samuel Amanya (2017-08-23). "Minister mutuuzo, Caroline Kamusiime win nrm party ticket". Uganda radio network. Retrieved 2020-04-17.
- ↑ "National resistance movement". NATIONAL RESISTANCE MOVEMENT.
- ↑ "Uganda and Rwanda officials disagree at body handover". The independent. 2018-05-28. Retrieved 2020-04-16.
- ↑ URN (2019-05-28). "Museveni sends shs 10m to Rwanda murder victim's family". Observer. Retrieved 2020-04-17.
- ↑ "Uganda and Rwanda officials disagree at body handover". The independent. 2018-05-28. Retrieved 2020-04-16.
- ↑ "Kamusiime Caroline - 2021 General Election - Visible Polls". visiblepolls.org (in Turanci). Retrieved 2023-02-10.
- ↑ "Kamusiime Caroline - Rukiga Woman MP By Election - Visible Polls". visiblepolls.org (in Turanci). Retrieved 2023-02-10.
- ↑ 11.0 11.1 11.2 11.3 11.4 "Parliament of Uganda members of the 10th parliament". Parliament of uganda. Retrieved 2020-04-16. Cite error: Invalid
<ref>tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ "Find an mp". Parliament of the republic of Uganda. Retrieved 2020-04-16.
- ↑ Olive Nakatude (2017-11-29). "6 more mps join legal committee". Uganda radio network. Retrieved 2020-04-17.