Cesc Fabregas

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Cesc Fabregas
Rayuwa
Haihuwa Arenys de Mar (en) Fassara, 4 Mayu 1987 (36 shekaru)
ƙasa Ispaniya
Karatu
Harsuna Yaren Sifen
Catalan (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa da association football coach (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Arenys de Mar (en) Fassara-
CE Mataró (en) Fassara1995-1997
  FC Barcelona1997-2003
  Spain national under-16 association football team (en) Fassara2002-200380
Arsenal F.C. Reserves (en) Fassara2003-2003
  Spain national under-17 football team (en) Fassara2003-2004147
Arsenal FC2003-201121235
  Spain national under-21 association football team (en) Fassara2004-2005128
  Catalonia national football team (en) Fassara2004-30
  Spain national under-20 football team (en) Fassara2005-200550
  Spain national association football team (en) Fassara2006-201611015
  FC Barcelona2011-20149628
Chelsea F.C.2014-11 ga Janairu, 201913815
  AS Monaco FC (en) Fassara11 ga Janairu, 2019-30 ga Yuni, 2022543
  Como 1907 (en) Fassaraga Augusta, 2022-ga Yuli, 2023170
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Nauyi 76.5 kg
Tsayi 179 cm
Kyaututtuka
Sunan mahaifi Cesc
cescfabregas.com
Cesc Fàbregas a wasan da suka fafata da maccabi

Francesc " Cesc " Fàbregas Soler ( Catalan pronunciation: [ˈsɛsk ˈfaβɾəɣəs] ; Spanish: [ˈfaβɾeɣas] ; an haife shi ne a hudu ga watan 4 Mayu 1987) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Sipaniya wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Seria B ta qasar Italiya Como .

Fàbregas ya zo ta La Masia a qasar sipaniya, makarantar matasa ta garinBarcelona, ya bar yana da shekaru shashidda kacal 16 lokacin da kulob din Arsenal na Premier a qasar burtaniya ya sanya hannu a watan Satumba shekarar dubu biyu da uku 2003. Bayan raunin da ya samu ga manyan 'yan wasan tsakiya a farkon lokacin kakar dubu biyu da hudu zuwa dubu biyu da biyar 2004–05, ya ci gaba da kafa kansa a cikin tawagar. Ya karya tarihin kungiyar da dama a cikin wannan tsari, inda ya samu suna a matsayin daya daga cikin ’yan wasa mafi kyau wanda suka iya sarrafa fasin a matsayinsa, kuma ya lashe kofin gasar FA a shekara ta dubu biyu da biyar 2005. Bayan tsawaita saga na canja wuri, Fàbregas ya bar London a ranar sha biyar 15 ga watan Agusta 2011 don komawa Barcelona a cikin yarjejeniyar da ta kai yuro miliyan talatin da biyar. A cikin shekaru uku da ya yi a Camp Nou, Fàbregas ya taka leda tare da Xavi da Andrés Iniesta kuma ya lashe gasar La Liga, da Copa del Rey, da FIFA Club World Cup, UEFA Super Cup da Spanish Super Cups guda biyu . Ya koma Landan ne a watan Yunin 2014 zuwa ga abokan hamayyar Arsenal na Chelsea kan kudi fan 30. miliyan, kuma a cikin shekararsa ta farko a can ya taimaka wajen tabbatar da nasarar cin kofin League da na Premier.

Cesc Fabregas

A duniya, Fàbregas ya fara buga wa tawagar kasar tasa wato Sipaniya wasa a watan Maris na shekarai dubu biyu da shidda 2006. Ya wakilci kasarsa a gasar cin kofin duniya ta FIFA shekarai dubu biyu da shidda 2006, UEFA Euro 2008, 2009 FIFA Confederations Cup, 2010 World Cup, Euro 2012, 2013 Confederations Cup, 2014 World Cup da Euro 2016 . Ya kasance babban jigo a nasarar da Spain ta samu a gasar cin kofin Turai a shekarai dubu biyu da takwas 2008 da 2012 da kuma nasarar da suka yi a gasar cin kofin duniya a 2010 inda ya ba da izinin cin kwallon da Andrés Iniesta ya ci a wasan karshe . A ranar 12 ga Oktoba, 2015, Fàbregas ya sami damar buga wa Spain wasa na 100 .

Cesc Fabregas

An haife shi a garin qaramar hukuma cikin kataloniya Arenys de Mar, Barcelona, Catalonia, zuwa Francesc Fàbregas Sr., wanda ke gudanar da wani qatan kamfani, da Núria Soler, mai kamfanin kek, Fàbregas ya goyi bayan qungiyar FC Barcelona tun lokacin yana dan yaro kuma ya tafi wurinsa. wasan farko lokacin yana da wata tare da kakansa. [1] Ya fara wasan kwallon kafa na qungiya din da CE Mataró kafin a sanya masa hannu akwantiragin makarantar matasa ta La Masia na Barcelona yana da shekaru goma a a shekarai alif dari tara da casain da bakwai 1997. [2] Rahotanni sun ce kocinsa na farko, Señor Blai, bai zabi Fàbregas ba domin buga wasa da Barcelona a kokarin boye shi daga masu leken asiri. [3] Wannan dabara, duk da haka, ta kasa jurewa qungiyar Barcelona na dogon lokaci, kuma Mataró ya ba da izini kuma ya ba yaran wato Fàbregas damar horar da Barcelona kwana ɗaya a mako. A ƙarshe Fàbregas ya shiga makarantar qungiyar Barcelona cikakken lokaci. Horon sa na farko shine dan wasan tsakiya na tsaro mai hidda fasissika yana wasa tare da sanannun sunaye irin su Gerard Piqué da Lionel Messi andreas inesta da xavi hernandez . Duk da cewa ya kasance dan wasan da ya fi zura kwallo a raga, wani lokaci ma yana zira kwallaye sama da guda talatin 30 a kakar wasa ta bana ga kungiyoyin matasa na kulob din, bai samu damar buga wasan farko a filin wasa na Camp Nou ba. [4] A lokacin da yake a makarantar matasa na qungiyar qwallan qafa ta Barcelona, Fàbregas ya bautar da kyaftin na Barcelona kuma mai lamba hudu Pep Guardiola, wanda daga baya zai ba Fàbregas rigarsa don ta'aziyya lokacin da iyayen Fàbregas suka rabu. [5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Francesc Fabregas: Spanish marvel blossoms out of the world of his mentors, The Independent, accessed 31 August 2010.
  2. Cuando todo era un sueño, ELPAÍS.com, accessed 16 May 2006
  3. Cesc Fàbregas faces the Barcelona Dream Team he left behind, The Guardian, 31 March 2010, accessed 18 September 2010.
  4. Cesc Fabregas, UEFA, accessed 23 May 2007.
  5. The one that got away, BBC Sport, accessed 1 June 2010.