Charles Uzo Azubuike
![]() | |||
---|---|---|---|
6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015 ← Nnanna Uzor Kalu - Ossy Prestige (en) ![]() District: Aba North/Aba South 60 | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a |
Charles Uzo Azubuike lauya ne kuma ɗan siyasa a Najeriya. Ya taɓa zama mamba mai wakiltar mazaɓar Obingwa ta yamma a majalisar dokokin jihar Abia. An naɗa shi mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abia daga shekarun 2007 zuwa 2011. [1] [2] [3] Ya taɓa zama mamba mai wakiltar Aba ta Arewa/Aba ta Kudu a majalisar wakilan Najeriya a majalisar wakilai ta 7 daga shekarun 2011 zuwa 2015 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP [4] [5] [2]
Tarihi da farkon rayuwarsa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Uzo Azubuike a jihar Abia, Najeriya. [6]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Azubuike ya yi karatun firamare da sakandare a jihar Abia. Ya halarci Jami'ar Jihar Abia (ABSU), inda ya samu digirin farko a fannin shari'a. [6]
Aikin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Uzo Azubuike ya riƙe muƙamai da dama a tsawon rayuwarsa ta siyasa. Ya kasance ɗan majalisar dokokin jihar Abia, ya wakilci mazaɓar Obingwa ta yamma, ya zama mataimakin kakakin majalisa, a majalisar dokokin jihar Abia daga shekarun 2007 zuwa 2011. [2] [6] Ya kasance ɗan majalisar wakilai daga shekarun 2011 zuwa 2015. An zaɓe shi don wakiltar mazaɓar tarayya ta Obingwa/Osisioma/Ugwunagbo. [4] Gwamna Okezie Ikpeazu ya naɗa shi kwamishinan noma na jihar Abia, inda ya yi aiki daga shekarun 2015 zuwa 2017. [7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Why people thought Reps wanted to impeach President Jonathan - Hon. Azubuike". Vanguard News (in Turanci). 2013-11-02. Retrieved 2024-12-28.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 eribake, akintayo (2013-12-21). "Abia 2015: It's the turn of Ukwa-Ngwa people—Hon. Azubuike". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-12-28. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ Agwu, Udoka (2023-03-08). "Ahiwe has the experience to turn Abia around quickly, Ex-deputy speaker, Azubuike, says". Businessday NG (in Turanci). Retrieved 2024-12-28.
- ↑ 4.0 4.1 "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nassnig.org. Archived from the original on 2015-10-02. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":1" defined multiple times with different content - ↑ "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-28.
- ↑ 6.0 6.1 6.2 Kashgain. "Uzo Azubuike: Biography, Family and Political Career". kashgain.net (in English). Retrieved 2024-12-28.CS1 maint: unrecognized language (link) Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":2" defined multiple times with different content - ↑ Grace, Ihesiulo (2017-11-14). "Ikpeazu swears in 27 new commissioners". DAILY TIMES Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-12-28.