Chidozie Kennedy Ibeh
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | 25 ga Yuni, 1976 (50 shekaru) |
| ƙasa | Najeriya |
| Karatu | |
| Makaranta |
Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu Jami'ar Jihar Abia Makarantar Koyan Lauya ta Najeriya |
| Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
Chidozie Kennedy Ibeh ɗan siyasar Najeriya ne kuma lauya. Shi ɗan majalisar dokokin jihar Imo ne mai wakiltar mazabar jihar Obowo.[1][2][3][4]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Chidozie Kennedy Ibeh a ranar 25 ga watan Yuni 1976. Ya kammala karatunsa na sakandare a ASCL Comprehensive Secondary School Kogi State kafin ya wuce digirin digirgir (LL.B Hons) a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu sannan ya yi digiri na biyu a fannin shari’a (LL.M) daga Jami’ar Jihar Abia, Uturu, Jihar Abia.
Fagen siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2010, an zabe shi kansila mai wakiltar Okenanlogho, a jihar Imo kuma a matsayin shugaban majalisar dokoki ta Obowo a 2011. A 2015, ya wakilci mazabar Obowo a majalisar dokokin jihar Imo. Ya taba zama mamba a kwamitin mika mulki na karamar hukumar Obawo, kuma mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin kwadago.
Ya kasance kakakin majalisar dokokin jihar Imo a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress har sai da ya yi murabus daga mukamin a shekarar 2022.[5]
Addini
[gyara sashe | gyara masomin]Kennedy Kirista ne.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ RT. HON. BARR. CHIDOZIE KENNEDY IBEH". Imo State House of Assembly. Retrieved 2024-12-09
- ↑ undefined candidate data for 2023 - Stears Elections". www.stears.co. Retrieved 2025-07-09
- ↑ RT HONOURABLE BARRISTER KENNEDY CHIDOZIE IBEH : CELEBRATING A LEADER OF SUBSTANCE AT 48*". IKEDURUAPCMEDIAHUB. Retrieved 2025-07-09
- ↑ Anyanwu, Ikechukwu (2022-03-08). "HOW RT. HON. BARR. KENNEDY CHIDOZIE IBEH RECORDED MILESTONE ACHIEVEMENTS IN 100 DAYS". AriseAfrika. Retrieved 2025-07-09
- ↑ Nwafor (2022-09-20). "Imo Assembly gets new Speaker". Vanguard News. Retrieved 2024-12-10