Jump to content

Chike Aniakor

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Chike Aniakor
Rayuwa
Haihuwa 1939 (86/87 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen, Ibo
Karatu
Makaranta Indiana University (mul) Fassara
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a painter (en) Fassara
Employers Jami'ar Najeriya, Nsukka

Chike C. Aniakor (an haife shi ranar 21 ga Agustan 1939) ɗan Najeriya ne mai fasaha, masanin tarihin fasaha, marubuci kuma mawaƙi. Ayyukansa suna mayar da hankali ne kan jigogi na falsafa, siyasa da addini waɗanda suka shafi al’ummar Igbo da kuma Yaƙin Basasar Najeriya.[1] An adana wasu daga cikin fitattun ayyukansa na fasaha a manyan gidajen adana kayan tarihi na duniya, ciki har da Smithsonian Institution, Gidan Tarihi na Fasaha na Ƙasa da ke Najeriya (Nigerian National Gallery of Art), da kuma Museum für Völkerkunde da ke Frankfurt a Jamus.

Aniakor fitaccen marubuci ne mai yawan wallafe-wallafe, inda ya rubuta littattafai da muƙalu sama da 75 a fannoni daban-daban na fasaha, tarihi da al’adu.

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Chike Cyril Aniakor a garin Abatete da ke Jihar Anambra a Gabashin Najeriya ranar 21 ga Agustan shekarar 1939.[2] Mahaifiyarsa ƙwararriyar mai zane-zanen Uli ce, wani salo na fasahar gargajiyar Igbo.[2] Tun yana ƙarami ya samu kusanci da al’adu da gargajiyar Igbo, lamarin da ya haɓaka sha’awarsa ga raye-raye, fasaha, bukukuwan gargajiya da kuma tsarin gine-ginen al’ummar Igbo.[3]

Daga shekarar 1960 zuwa 1964, Aniakor ya yi karatu a Nigerian College of Arts, Science, and Technology da ke Zariya a Jihar Kaduna, wadda daga baya aka sauya sunanta zuwa Ahmadu Bello University, Zariya. A nan ne ya samu digiri na farko a fannin zanen fasaha (Painting).[2] Daga baya ya ci gaba da karatun digirgir a Indiana University Bloomington, inda ya samu digirin digirgir na biyu (Master’s degree) a shekarar 1974 da kuma digirin digirgir na uku (Doctorate) a tarihin fasaha a shekarar 1978.[4]

A lokacin da yake a Jami’ar Indiana, an nuna zane-zanensa da waƙoƙinsa a nune-nunen fasaha da dama, abin da ya ba shi karɓuwa a idon jama’a tare da samun tallafin karatu da lambobin yabo na ilimi, ciki har da Rockefeller Award.[5] Bayan kammala karatunsa, ya koyar a jami’o’i daban-daban kamar Southern University da ke New Orleans, UCLA da kuma Howard University.[2]

Tun daga shekarun 1970, Aniakor ya koyar da fasaha da tarihin fasaha a University of Nigeria, Nsukka (UNN), a Jihar Enugu. A can ne ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar Nsukka, wadda daga baya ta shahara saboda amfani da salon fasahar Uli na gargajiyar Igbo.

Haka kuma, ya kasance daga cikin waɗanda suka kafa sashen fasaha na jami’ar, wanda ya samu yabo saboda ƙwarewar malamai da ɗalibansa, tare da gabatar da ayyukan masu fasahar jami’ar ga dandamalin fasaha na duniya.[6]

  1. "Imago Mundi Collection". imagomundicollection.org.
  2. 1 2 3 4 Nwafor, Okechukwu (2020). "Chike C Aniakor: The The Community and a Congregation of Figural Elements". African Arts. 4: 58–67.
  3. Jegede, Dele (1997). New Traditions from Nigeria: Seven Artists of the Nsukka. Smithsonian Institution Press. pp. 2–109.
  4. Kelly, Bernice M. (1993). Nigerian Artists: A Who's Who and Biography. Hans Zell Publishers. pp. 118–120.
  5. Wole, Oloidi (2014). "Chike Aniakor: Master of Poetic Lines". Global Journal of Social Sciences. 13: 31–38 via AJOL.
  6. "Visionary Artists / The University of Nigeria, Nsukka". africa.si.edu. Archived from the original on 2025-03-28.