Chinwe Nwaebili
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Jahar Anambra, | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Karatu | |||
| Harsuna | Harshen, Ibo | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | All Progressives Grand Alliance | ||
Chinwe Nwaebili ita ce tsohuwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Anambra, Jihar Anhambra, Najeriya. An yi mata laƙabi da Rt. Hon. Barr . Gimbiya Chinwe Nwaebili. Ta kasance kakaki mace ta biyu a Majalisar Dokokin Jihar Anambra. [1] Kafin ta zama Kakakin Majalisar Dokoki, Rt. Hon. Chinwe Nwaebili ta jagoranci kwamitoci daban-daban guda huɗu a Majalisar Dokokin Jiha.[2] Ta kasance 'yar Jam'iyyar siyasa ta All Progressive Grand Alliance (APGA) amma a cikin 2021, ta shiga Jam'iyyar siyasar African Action Congress (AAC) kuma ta yi takara a matsayin Mataimakiyar Gwamna na Jihar Anambra tare da Dr. Chidozie Nwankwo a matsayin Gwamna mai zuwa. Ta sanar da niyyarta na ta tsaya takarar Majalisa ta Tarayya ta Ogbaru a babban zaɓen 2019 a ƙarƙashin APGA .
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Hon. Chinwe ta fito ne daga karamar hukumar Ogbaru ta Jihar Anambra. Ta auri marigayi Prince Azubuike Patrick Nwaebili wanda aka gudanar da bikin tunawa dashi na shekara ta 10 a Asaba, Jihar Delta. [3]
Ayyukan siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Chinwe Nwabili ta kasance memba na Jam'iyyar siyasa ta APGA, ta inda ta fito a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Anambra. A cikin shekarar 2021 ta bar APGA kuma ta shiga Jam'iyyar siyasa ta AAC. Ta zama abokiyar takarar Dr. Chidozie Nwankwo a yakin neman zaɓe na Gwamna a Jihar Anambra. [4] A shekarar 2009, a lokacin bita na Canjin yanayi ga 'yan wasan gwamnati, wanda PASDO ta shirya, Hon. Chinwe ta ba da gudummawa ga damuwa game da muhalli.[5] An ce ta karfafa matasa a cikin al'ummarta.[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Donney, Donyoh (2015-06-12). "Mmaduagwu Emerges 3rd Female Speaker Of Anambra Assembly". Channels Television (in Turanci). Retrieved 2025-01-06.
- ↑ Nation, The (2014-10-10). "I get passes from men but my status scares them -Anambra Speaker Chinwe Nwaebili". The Nation Newspaper (in Turanci). Retrieved 2025-01-06.
- ↑ "OCI Foundation's National Champion joins former Anambra State House Speaker, Princess Chinwe Nwaebili, on the 10th anniversary of her late husband (Asaba, Nigeria; 14/8/22)". OCI Foundation | Onyebuchi Chris Ifediora (in Turanci). 2022-08-15. Retrieved 2025-01-06.
- ↑ Augustine, Saint (2021-09-23). "Dr. Chidozie Nwankwo: The Governor Anambra deserve in a time like this". Prime Time Reporters (in Turanci). Retrieved 2025-01-06.
- ↑ "Environment: Climate Change and Biodiversity Conservation | PASDO" (in Turanci). Retrieved 2025-01-06.
- ↑ Festus Chimezie Ajeli and A. U. Igwe (2023). "THE PLACE OF INDIGENOUS EFFORTS TOWARDS THE POLITICAL AND SOCIO-ECONOMIC GROWTH OF OGBARU, 1970-2018". AMAMIHE: Journal of Applied Philosophy. 21 (4): 337–349 – via amamihe.[permanent dead link]