Chris Adighije
Chris Iheanyichukwu Adighije ya kasance ɗan siyasan Najeriya ne sannan kuma ɗan majalisa. Ya taɓa zama sanata mai wakiltar mazaɓar Abia ta tsakiya a majalisar wakilai ta ƙasa. [1]
Rayuwar farko da aiki
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Adighije a ranar 22 ga watan Maris, 1945, a jihar Abia. [2] Ya yi digirin farko na Kimiyya (B.Sc) a fannin Geology a Jami’ar Ibadan a shekarar 1973. Daga nan ya samu digirin digirgir (MPhil) a shekarar 1976 da digirin digirgir (PhD) a shekarar 1978, dukkansu a jami'ar Ibadan. [3]
Adighije ya riƙe muƙamai daban-daban a lokacin aikinsa. Ya taɓa zama kwamishinan gwamnatin tarayya na jihar Abia a hukumar tattara kuɗaɗen shiga da hada-hadar kuɗi (RMAFC) daga shekarar 2010 zuwa 2015. [4] [5] Ya zama Sanata mai wakiltar Abia ta tsakiya daga shekarun 2003 zuwa 2007. [6] Ya kuma kasance ma'ajin jam'iyyar National Republican Convention (NRC) daga shekarun 1990 zuwa 1992 da kuma sakataren jam'iyyar National Congress (NNC) daga shekarun 1988 zuwa 1989. [7]
A watan Yuli 2020, an naɗa shi Pro-Chancellor kuma Shugaban Majalisar a Jami'ar Tarayya Lokoja. [8] [9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Idachaba, Eleojo (2023-05-12). "David Jemibewon, Chris Adighije: Where are they now?". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2024-12-29.
- ↑ Godfrey, Chimezie (2024-03-24). "Sen Adighie @79: The best birthday gift I want is a new Nigeria". News Diary Online (in Turanci). Retrieved 2024-12-29.
- ↑ ".:: Abridged Profile of Senator Chris Adighije | Federal University Lokoja". fulokoja.edu.ng. Retrieved 2024-12-29.
- ↑ eribake, akintayo (2015-12-17). "Abia political stakeholders urge Buhari to reappoint Adighije at RMFAC". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-12-29.
- ↑ vanguard (2016-12-12). "Recession: Nigerians now more ingenious, creative — Sen. Adighije". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-12-29.
- ↑ Emeruwa, Chijindu (2019-05-29). "7th Abia Assembly: Senator Adighije explains why Ikwuano/Umuahia should produce next Speaker". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2024-12-29.
- ↑ Telegraph, New (2022-03-21). "APC Convention: There is revolution over zoning – Adighije". New Telegraph (in Turanci). Retrieved 2024-12-29.
- ↑ "Abia APC Congratulates Sen. Chris Adighije over his appointment as Pro-Chancellor, Federal University Lokoja - News Mirror" (in Turanci). Retrieved 2024-12-29.
- ↑ OHAFIATV (2020-07-17). "Buhari Appoints Senator Chris Adighije As Pro Chancellor, Federal University Of Lokoja (FULOKOJA)". OHAFIATV (in Turanci). Retrieved 2024-12-29.[permanent dead link]