Jump to content

Cristiano Ronaldo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Christiano Ronaldo)
Cristiano Ronaldo
Rayuwa
Cikakken suna Cristiano Ronaldo dos Santos Aveiro
Haihuwa Funchal (mul) Fassara, 5 ga Faburairu, 1985 (40 shekaru)
ƙasa Portugal
Mazauni Funchal (mul) Fassara
Torino
Lisbon
Manchester
Madrid
Manchester
Harshen uwa Portuguese language
Ƴan uwa
Mahaifi José Dinis Aveiro
Mahaifiya Maria Dolores dos Santos Aveiro
Ma'aurata Georgina Rodriguez
Irina Shayk (en) Fassara
Yara
Ahali Elma dos Santos Aveiro (en) Fassara, Hugo Aveiro (en) Fassara da Kátia Aveiro (en) Fassara
Ƴan uwa
Karatu
Harsuna Portuguese language
Yaren Sifen
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa, fashion entrepreneur (en) Fassara da model (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Portugal national under-15 football team (en) Fassara2001-200197
  Portugal national under-17 football team (en) Fassara2001-200275
  Sporting CP2002-2003253
  Portugal national under-21 football team (en) Fassara2002-2003103
  Manchester United F.C.2003-200919684
  Portugal national under-20 football team (en) Fassara2003-200351
  Portugal men's national football team (en) Fassara2003-226143
  Portugal Olympic football team (en) Fassara2004-200432
  Real Madrid CF2009-2018292311
  Juventus FC (en) Fassara2018-26 ga Augusta, 20219881
  Manchester United F.C.27 ga Augusta, 2021-22 Nuwamba, 20224019
Al-Nassrga Janairu, 2023-8684
 
Muƙami ko ƙwarewa wing half (en) Fassara
Ataka
Lamban wasa 7
28
Nauyi 85 kg
Tsayi 185 cm
Kyaututtuka
Ayyanawa daga
Sunan mahaifi CR7, El Comandante, D7OS, Míster Champions da El Bicho
IMDb nm1860184
cristianoronaldo.com
Cristiano Ronaldo
hoton ronaldo
hoton gunkin ronaldo
hoton Rinaldo a Madrid
ronaldo a juventus
sa hanun Rinaldo
hoton ronaldo
hoton a saudia
Hoton ronaldo a training
Ronaldo
Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo dos Santos Aveiro (an haife shi a ranar 5 ga watan Fabrairu, a shekara ta alif dari tara da tamanin da biyar 1985)[1] ya kasance shahararren ɗan'wasan ƙwallon ƙafana ƙasar Portugal ne wanda a halin yanzu yake buga wasa a kulub ta Al nassr dake ƙasar Saudiya.[2] Ana daukarsa a matsayin dan sa mafi shahara a duniya na kowanne lokaci, Wanda a yanzu haka ya lashe lamban yabo na dan wasan shekara wato Ballon d'Or har sau biyar, kuma lambar yabo ta European Golden Shoe har sau hudu, wanda yafi kowanne bature lashe kyautar,a matsayinsa na dan wasa ya lashe kofuna 32, wanda suka hada da kofunan gida guda bakwai, Kofin Zakarun Turai (UEFA), da kuma kofin UEFA European Championship guda daya. Ronaldo ya ajiye tarihin wanda yafi kowa fara wasanni (183), kwallaye (140), wanda ya bada akaci (42) a wasannin Zakarun Turai (UEFA), ya jefa kwallaye (14) a gasar Europa Championship, kwallaye (117) wa kasarsa, sannan kuma ya buga wasannin kasa da kasa guda (191). Ronaldo na daya daga cikin tsirarun 'yan wasan kwallon kafa da suka buga wasannin fiye da guda 1,100 da kwallaye 800 a sashin kasa da kuma kulab.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi da kuma girma a Madeira, Ronaldo ya fara wasan ƙwallon ƙafa tare da kungiyar Sporting CP, kafin ya rattaba hannu tare da Manchester United a shekara ta 2003, yana ɗan shekara 18, ya lashe Kofina a farkon kakar sa. ya kuma ci nasarar lashe kofunan Premier uku a jere, Champions League da FIFA Club World Cup; yana dan shekara 23, ya lashe Ballon d'Or na farko. Ronaldo ya kasance mafi tsada a lokacin da ya sanya hannu a Real Madrid a shekara ta 2009,a canja wurin da ya kai (€ 94 miliyan) (£ 80 million), in da ya lashe kofuna 15, ciki har da kofin La Liga biyu, Copa del Rey biyu Gasar Zakarun Turai hudu, sannan ya zama dan wasan da ya fi kowa zira kwallaye a kulob din. Har ila yau, ya gama zama na biyu na Ballon d'Or sau uku, bayan Lionel Messi (wanda ake tunanin zai zama abokin hamayyarsa, kuma ya lashe Ballons d'Or sau biyu a shekara ta 2013 da shekara ta 2014,sannan kuma a shekara 2016, da shekara ta 2017 ,A cikin shekara ta 2018, Ronaldo ya rattaba hannu ga Juventus a musayar wanda darajarsa ta kai ( € 100 miliyan ) (£ 88 miliyan), mafi tsada ga kulob din Italiya kuma mafi tsada ga ɗan wasa sama da shekaru talatin 30, Ya lashe kofunan Serie A guda biyu, Supercoppe Italiana biyu da Coppa Italia, kafin ya koma Manchester United a shekara ta 2021 a inda ya zauna na rabin kaka a Manchester United sannan ya rattabawa Al nassr a shekara ta 2023 a watan junairu. (Ihayatu (talk) 08:49, 31 Mayu 2023 (UTC))[3]

Tauraron ɗanwasa Cristiano Ronaldo ya fantsama harkar shirya finafinai tare da haɗin gwiwar kamfanin UR-Marv da suka kafa tare da mai bayar da umarni Mathew Vaughn. Wannan yunƙuri nasa ya tabbatar da sha'awar fara sabuwar sana'a da ɗan ƙasar Portugal ɗin mai shekara 40 ya bayyana a baya da cewa "harka ce da ke burge ni yayin da nake neman shiga wasu harkokin kasuwnacin". Wata sanarwa da Ronaldo ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ta ce tuni suka shirya zango biyu na wani fim tare da Vaughn, wanda za a fitar da bayanai kansu nan gaba, har ma sun fara aiki kan zango na uku na fim ɗin. Matthew Vaughn sananne ne a masana'antar, inda ya shirya finafinai "Kick-Ass" da "Kinsman", kuma ya ce ya zaƙu game da haɗakar tasu da Ronaldo. "Cristiano ya samar da labarai yayin da yake taka leda waɗanda ban taɓa tunani ba. Muna da zimmar ƙayatar da 'yankallo tare da shi," kamar yadda sanarwar ta ambato shi yana faɗa. Baya ga shigarsa harkar fim, Ronaldo na ci gaba da faɗaɗa harkokinsa a wajen wasanni. Ya zuba jari a kafar yaɗa labarai ta Portugal mai suna Medialivre da kuma kafa tasharsa ta YouTube mai suna UR Cristiano a 2024, yayin da yake son cigaba da ɗaukaka sunansa a duniya. ‎Cristiano Ronaldo, mai shekara 39, ya shawarci ƙungiyarsa ta Al-Nassr da ke Saudiyya da ta ɗauki Kevin de Bruyne, idan kwantiragin ɗan wasan na tsakiya na Belgium mai shekara 33 ya ƙare da Manchester City a bazara mai zuwa. (Mundo Deportivo) ‎Manchester United na son ɗaukar kociyan Bayer Leverkusen Xabi Alonso domin maye gurbin Erik ten Hag, kuma a shirye ƙungiyar ta Old Trafford take ta jira tsohon ɗan wasan na tsakiya na Livepool har zuwa bazara. (Todofichajes) Manchester United, na son sayen ɗan bayan Aston Villa Pau Torres kuma ashirye take ta taya ɗan wasan na Sifaniya mai shekara 27, kusa da fam miliyan 42. (Fichajes ) ‎Manchester United ta samu amincewar hukumar gasar Premier, ta sayen matashin ɗan wasa Chido Obi-Martin, wanda ya taka wa Ingila da Denmark leda a matakin wasan matasa. Shi ma ɗan wasan mai shekara 16 ya tabbatar da tafiyar tasa daga Arsenal a shafinsa na sada zumunta da muhawara. (Manchester Evening News) ‎Ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiyya tana son ɗaukar Mohamed Salah, mai shekara 32, da abokin wasansa a Liverpool Virgil van Dijk, mai shekara 33, idan kwanriraginsu ya ƙare a Anfield a ƙarshen kaka. (Caught Offside) Robert Lewandowski, na Poland mai shekara 36, yana da zaɓin tsawaita kwantiraginsa da Barcelona har zuwa bayan bazara mai zuwa, idan ya cika wasu ƙa'idoji, wadanda kuma ake sa ran ya cimma. (Sport ) Barcelona na duba yuwuwar tura matashin ɗanwasanta na Sifaniya Ansu Fati mai shekara 21 wanda ya yi zaman aro a Brighton a kakar da ta wuce, wani aron a watan Janairu. (Sport). Ɗan wasan Ingila mai kai hari Eddie Nketiah, mai shekara 25, ya ce ya bar Arsenal ne ya tafi Crystal Palace a bazara, domin samun damar taka leda sosai da kuma bunƙasa.'' (Independent)[4]

(Ihayatu (talk) 08:49, 31 Mayu 2023 (UTC))

  1. Hamilton, Nigel (23 September 2004). Chisholm, Hugh (1866–1924), journalist and editor of the Encyclopaedia Britannica. Oxford Dictionary of National Biography. Oxford University Press.
  2. "Latest SUN Revision". Europhysics News. 19 (7–8): 104–104. 1988. doi:10.1051/epn/19881907104. ISSN 0531-7479.Cristiano Ronaldo - Latest News on Man Utd ace - The Sun
  3. "Ronaldo is coming home!". www.manutd.com. Retrieved 19 November 2022.
  4. K