Christina Koch
| Rayuwa | |
|---|---|
| Cikakken suna | Christina Marie Hammock |
| Haihuwa | Grand Rapids (mul) |
| ƙasa | Tarayyar Amurka |
| Karatu | |
| Makaranta | North Carolina State University (en) North Carolina School of Science and Mathematics (mul) NASA Academy (en) |
| Harsuna | Turanci |
| Sana'a | |
| Sana'a | astronaut (en) |
| Employers | Gudanar da Tsarin Ruwa da Ruwa na ƙasa |
| Kyaututtuka | gani
|
| IMDb | nm8933484 |
Christina Hammock Koch (an haife ta a Hammock; Janairu 29, 1979) injiniya ce 'yar Amurka kuma 'yar sama jannatin NASA. A lokacin doguwar tafiyarta zuwa Tashar Sararin Samaniya ta Duniya a 2019–2020, ta yi tafiyar farko ta mata ta sararin samaniya kuma ta kafa tarihi na mace ta farko da ta yi tsawon tafiyar sararin samaniya. A shirin Artemis II a watan Afrilun 2026, wanda shine ya kafa tarihi na mafi nisan da mutum ya yi daga Duniya zuwa Duniyar Wata, Koch ta zama mace ta farko a tawagar da ta tafi sararin samaniya izuwa duniyar wata.
Kafin ta fara aiki da hukumar NASA, Koch ta yi aiki a Cibiyar Jiragen Sama ta Goddard kuma ta kasance shugabar tashar jiragen sama ta Hukumar Kula da Teku da Yanayi ta Amurka.
Rayuwar Farko da Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Christina Hammock a ranar 29 ga Janairu, 1979, a Grand Rapids, Michigan,[1][2] ta girma tare da iyayenta, Barbara Johnsen[lower-alpha 1] na Frederick, Maryland, da Ronald Hammock na Jacksonville,[3] a Jacksonville, North Carolina.[4] Tun tana ƙarama, ta ke sha'awar son zama ƴar sama jannati.[5]
A shekarar 1999, Koch ta shiga shirin musayar ɗalibai a Jami'ar Ghana, Legon, inda ta yi karatun kimiyyar taurari. Ta kammala makarantar sakandare a Makarantar Kimiyya da Lissafi ta North Carolina da ke Durham a shekarar 1997. Sannan ta je Jami'ar Jihar North Carolina da ke Raleigh kuma ta sami digirin farko na Kimiyya a fannin injiniyan lantarki da kimiyyar lissafi a shekarar 2001. Ta kuma sami digiri na biyu na Kimiyya a fannin injiniyan lantarki a shekarar 2002.[6][3] A shekarar 2001, ta kammala wani shirin NASA Academy a Cibiyar Jiragen Sama ta Goddard.[3]
Bincike da Horarwa
[gyara sashe | gyara masomin]
Koch tana da gogewa a fannin haɓaka kayan aikin kimiyyar sararin samaniya da injiniyan kimiyya. A matsayinta na injiniyan lantarki a dakin gwaje-gwaje na sararin samaniya na Goddard Space Flight Center (GSFC) na NASA don Kimiyyar taurari mai binciken matsanancin kuzari a sararin samaniya, ta yi aiki a fannonin kan kayan aikin kimiyya ga hukumar NASA da yawa waɗanda ke nazarin ilmin taurari da ilmin sararin samaniya.[3] A wannan lokacin, ta kuma koyar a matsayin memba na malamai a Kwalejin Montgomery da ke Maryland, inda ta jagoranci kwas ɗin dakin gwaje-gwaje na kimiyyar lissafi.[3]
Daga 2004 zuwa 2007, Koch ta yi aiki a matsayin mai bincike a Shirin Antarctic-(wata nahiyar ce da ke gefen kudu da duniya/South Pole, Ita ce nahiyar da ta fi kowacce sanyi, bushewa, da iska a duniya) na Amurka, inda ta shafe sama da shekaru uku a yankunan Arctic-(Yankin Arewa da duniya) da Antarctic-(Yankin Kudu da duniya).[3][7] Ta kammala kakar hunturu a Tashar Amundsen-Scott South Pole, inda yanayin zafi ya ragu zuwa −111 °F (−79.4 °C),[7] kuma ta yi aiki a lokacin bazara a Tashar Palmer. Yayin da take Antarctica, ta kasance cikin ƙungiyoyin kashe gobara da ƙungiyoyin bincike da ceto don tekuna da ƙanƙara.[3] Ta bayyana lokacin zamanta da ta yi a Kudancin Pole a matsayin mai matuƙar wahala ko ƙalubale[7], tana mai bayyana cewa hakan ya ƙunshi watanni ba tare da hasken rana ba, ƙarancin ma'aikata, babu jigilar wasiku ko abinci sabo, da kuma magance warewa da rashin sabbin abubuwan da ke haifar da ji.[8]
Tsakanin 2007 da 2009, Koch ta yi aiki a matsayin injiniyan lantarki a Dakin Gwaji na Jami'ar Johns Hopkins Applied Physics a Sashen Sararin Samaniya, tana mai da hankali kan kayan aikin kimiyyar sararin samaniya don ayyukan NASA, ciki har da Juno da Van Allen Probes.[3] Ta kuma yi aiki a Palmer Station da ke Antarctica kuma ta shafe lokacin sanyi da dama a Summit Station da ke Greenland.[3] A shekarar 2012, ta shiga Hukumar Kula da Teku da Yanayi ta Ƙasa (NOAA), da farko a matsayin injiniyan fili a Baseline Division Monitoring Division da ke Barrow, Alaska (yanzu Utqiaġvik), kuma daga baya ta yi aiki a matsayin shugabar tasha a Cibiyar Kula da Jiragen Sama ta Amurka.[3]
Ayyukan Ƴan Sama Jannati
[gyara sashe | gyara masomin]Koch ta kammala shirin NASA Academy a GSFC a shekarar 2001. Ta yi aiki a matsayin injiniyan lantarki a GSFC daga 2002 zuwa 2004.[9]
A watan Yunin 2013, NASA ta zaɓi Koch don zama wani ɓangare na ƙungiyar 'Yan Samari ta 21. Ta kammala samun horo a watan Yulin 2015, don haka ta shirya don ayyukan sararin samaniya da ke tafe.[10] Horarwar ta ta haɗa da koyo game da Tashar Sararin Samaniya ta Duniya, hanyoyin tafiya a sararin samaniya, na'urorin robot, lafiya da motsa jiki, tuƙa jirage samfurin T-38, da ƙwarewar rayuwa a cikin ruwa da daji don tsira da rai.[3]
Expeditions 59-61
[gyara sashe | gyara masomin]
A ranar sha hudu 14 ga Maris, 2019, Koch ta tafi sararin samaniya. Ta yi tafiya a cikin wani jirgin sama mai suna Soyuz MS-12. Ta tafi tare da Aleksey Ovchinin da Nick Hague. Sun je Tashar Sararin Samaniya ta Duniya. Sun zauna a can don shirin Expeditions 59, 60, da 61.[11]
An yi niyyar Koch ta yi tafiyarta ta farko ta sararin samaniya a ranar 29 ga Maris. Da zai zama tafiyar mace ta farko (a sararin sama) tare da Anne McClain. Amma saboda matsalolin girman kayan sararin samaniya, an maye gurbin McClain da Hague.[12] Daga baya, Koch ta zama mace da ta yi tafiyar sararin samaniya ta farko a ranar 18 ga watan Oktoba. Sun yi aiki a kan tsarin wutar lantarki na tashar sararin samaniya da kayan aikin kimiyya.[13][14][15] Koch da Meir sun yi wasu tafiyar sararin samaniya guda biyu ta mata kawai a watan Janairun 2020.[16]
A ranar 17 ga watan Afrilu, 2019, an tsawaita aikin Koch zuwa Fabrairun 2020 saboda canje-canje a shirin NASA. Ta dawo a doron Duniya a ranar 6 ga Fabrairu bayan ta kasance a sararin samaniya na tsawon kwanaki 328. Wannan shine mafi tsayin tafiyar sararin samaniya da wata mace ta taɓa yi a duniya, wanda ya doke tarihin Peggy Whitson na kwanaki 289.[17] Tsawon zamanta yana taimaka wa masana kimiyya su koyi yadda sararin samaniya ke shafar mata a zahiri, a hankali, da kuma a fannin halitta.[18][19][20] A lokacin da take a saman sararin samaniya, ta bayar da gudummawa-(editing) ta farko (da aka taɓa yi) a shafin Wikipedia daga sararin samaniya.[21][22]
Artemis II
[gyara sashe | gyara masomin]
An zabi Koch don zama wani ɓangare na shirin Artemis na NASA.[23] A ranar 3 ga Afrilu, 2023, an sanar da ita a matsayin memba na ma'aikatan Artemis II. An ƙaddamar da aikin a ranar 1 ga watan Afrilu, 2026, kuma an yi ta yawo a duniyar wata a ranar 6 ga Afrilu, 2026.[24][25][26] Sun yi tafiya mil 6,400 bayan gefen wata mai nisa sannan suka dawo Duniya a ranar 10 ga Afrilu, 2026.[27][28] Ita ce mace ta farko da ta bar ƙasan sararin samaniya ta je kusa da Wata.[29][30] Ta tafi tare da 'yan saman jannatin NASA; Reid Wiseman da Victor Glover, da Canadian Space Agency astronaut Jeremy Hansen.[27]
Rayuwar Kanta
[gyara sashe | gyara masomin]Koch tana zaune a Texas tare da mijinta, Bob, wanda injiniya ne a fannin yanayin ƙasa.[31][32][33] Sun haɗu a shekarar 2013 lokacin da Christina ke binciken Samoa ta Amurka.[34]
Abin sha'awarta-(abinda ta fi so) shine hawan igiyar ruwa, hawan dutse da kankara, shirye-shirye, hidimar al'umma, gasar iyon ruwa, wasan yoga, aikin katako, ɗaukar hoto, da tafiye-tafiye.[35][36] Koch kuma tana son ƙungiyoyin wasanni na Philadelphia kuma ta raba hotunanta da ta ɗauka tana kallon Phillies da Eagles a kan jirgin ruwa na ISS.[37]
Kyauta da girmamawa
[gyara sashe | gyara masomin]Koch ta sami kyaututtuka da yawa. Ta sami kyautar NASA Group Achievement Award don Juno Mission's Jupiter Particle Detector a shekarar 2012. Ta kasance cikin waɗanda aka zaɓa don ƙirƙirar shekarar Jami'ar Johns Hopkins a shekarar 2009. Ta sami lambar yabo ta Winter-Over a shekarar 2005. Ta kuma sami lambar yabo ta NASA Group Achievement Award don na'urar auna X-ray Spectrometer ta Suzaku Mission a shekarar 2005. Ta kasance ƙwararriya ƴar sama jannati daga 2000 zuwa 2001.[3]
A watan Disamba na 2020, Koch ta sami digirin girmamawa na Doctor of Sciences daga Jami'ar Jihar North Carolina.[38]
An sanya sunanta a matsayin ɗaya daga cikin mutane 100 mafiya tasiri a shekarar 2020.[39]
Bayanan Kula
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Name at birth was Barbara Homrich
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "NASA Astronaut Christina Koch". NASA.
- ↑ Raven, Benjamin (March 8, 2019). "NASA's first all-women spacewalk features Michigan native". mlive.com (in Turanci). Retrieved March 18, 2019.
- 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 Whiting, Melanie (November 27, 2015). "Christina Hammock Koch NASA Astronaut". NASA. Retrieved March 29, 2019.
- ↑ Rupinta, Amber (February 26, 2019). "NASA astronaut, NC State grad Christina Koch ready for first space flight in March". ABC11 Raleigh-Durham (in Turanci). Retrieved March 18, 2019.
- ↑ Daily News Staff. "Jacksonville astronaut will 'carry the dreams of everyone' to space". The Daily News (in Turanci). Archived from the original on March 30, 2019. Retrieved March 18, 2019.
- ↑ "Alumna Astronaut Prepares to Launch to the ISS • Electrical and Computer Engineering". NC State University | Electrical and Computer Engineering (in Turanci). February 20, 2019. Retrieved April 19, 2019.
- 1 2 3 Herman, Danielle (July 30, 2018). "N.C. State grad joins space race". Business North Carolina (in Turanci). Retrieved March 18, 2019.
- ↑ "Antarctica Provides ICE to Study Behavior Effects in Astronauts – SpaceRef". SpaceRef. September 13, 2016. Archived from the original on June 6, 2020. Retrieved March 18, 2019.
- ↑ "Five Facts about Space Camp Astronaut Alumna Christina Koch!". Space Camp. U.S. Space and Rocket Center. March 8, 2019. Archived from the original on April 19, 2019. Retrieved April 19, 2019.
- ↑ "NASA's Newest Astronauts Complete Training". NASA. July 9, 2015. Archived from the original on April 4, 2019. Retrieved July 10, 2015.
- ↑ Gebhardt, Chris (March 14, 2019). "Soyuz MS-12 docks with the Space Station". NASASpaceflight.com.
- ↑ Berger, Eric (March 26, 2019). "It's unfortunate NASA canceled the all-female EVA, but it's the right decision". Ars Technica (in Turanci).
- ↑ "NASA Astronauts Spacewalk Outside the International Space Station on Oct. 18". NASA. October 18, 2019. Retrieved October 18, 2019 – via YouTube.
- ↑ "Voor het eerst maakt vrouwelijk duo ruimtewandeling bij ISS" [For the first time a female duo is taking a space walk at ISS]. nu.nl (in Holanci). October 18, 2019.
- ↑ Garcia, Mark (October 18, 2019). "NASA TV is Live Now Broadcasting First All-Woman Spacewalk". NASA Blogs. NASA. Retrieved October 18, 2019.
- ↑ Rincon, Paul (February 6, 2020). "New female space record for Nasa astronaut". BBC News (in Turanci). Retrieved February 6, 2020.
- ↑ Northon, Karen (February 6, 2020). "Record-Setting NASA Astronaut, Crewmates Return from Space Station". NASA. Retrieved February 12, 2020.
- ↑ Northon, Karen (April 16, 2019). "NASA Announces First Flight, Record-Setting Mission". NASA. Retrieved April 19, 2019.
- ↑ "NASA astronaut to set record for longest spaceflight by a woman". Agence France Press (in Turanci). Archived from the original on April 17, 2019. Retrieved April 17, 2019.
- ↑ Dunn, Marcia (April 17, 2019). "US astronaut to spend 11 months in space, set female record". AP NEWS. Retrieved April 19, 2019.
- ↑ Wikipedia [@wikipedia.org] (November 17, 2025). "On this day in 2019, NASA astronaut Christina Koch made the first edit to a Wikipedia article from outer space". Retrieved April 2, 2026 – via Bluesky.
- ↑ Brown, Alyssa (10 April 2026). "From Orbit to Open Source: How Wikipedia Shapes Scientific Progress". datascience.virginia.edu. Retrieved 11 April 2026.
- ↑ "NASA: The Artemis Team". NASA. Retrieved December 10, 2020.
- ↑ Low, Lauren E. (2026-04-01). "Liftoff! NASA Launches Astronauts on Historic Artemis Moon Mission". NASA. Retrieved 2026-04-02.
- ↑ Donaldson, Abbey A. (2024-12-05). "NASA Shares Orion Heat Shield Findings, Updates Artemis Moon Missions". NASA. Retrieved 2024-12-05.
- ↑ Berger, Eric (2025-09-23). "NASA targeting early February for Artemis II mission to the Moon". Ars Technica (in Turanci). Retrieved 2025-12-16.
- 1 2 Maidenberg, Micah (April 3, 2023). "NASA Names Artemis II Crew for Mission to Fly by Moon in 2024". WSJ.com. Retrieved April 3, 2023.
- ↑ Watch Live: NASA announces astronauts for Artemis II moon flyby mission. YouTube. CBS News. April 3, 2023. Retrieved April 5, 2023.
- ↑ Staff, T. M. Z. (April 13, 2026). "Astronaut Christina Koch's Joyful Dog Reunion After Artemis II, on Video". FOX 22/ABC 7.
- ↑ Melimopoulos, Elizabeth. "NASA's Artemis II astronauts splash down on Earth after lunar mission". Al Jazeera.
- ↑ Cite error: Invalid
<ref>tag; no text was provided for refs named ":1". - ↑ Carter, Jamie. "Meet The First Female Astronaut To Go On A Moon Mission". Forbes (in Turanci). Archived from the original on 2026-04-01. Retrieved 2026-04-03.
- ↑ "Astronaut craves salsa and surf after record 11 months aloft". AP News (in Turanci). 2020-01-29. Retrieved 2026-04-03.
- ↑ Samfuri:Cite podcast
- ↑ "Resident Extreme – NASA" (in Turanci). Retrieved 2026-04-06.
- ↑ "Christina Koch – NASA" (in Turanci). Retrieved 2026-04-06.
- ↑ Simpson, Ariel (April 9, 2026). "Artemis II astronaut Christina Koch is a big Philly sports fan — and even watches games from space". Philadelphia Inquirer. Retrieved 2026-04-14.
- ↑ Peeler, Tim (19 November 2020). "Launching the Next Generation". News. North Carolina State University. Archived from the original on 16 January 2023. Retrieved 4 April 2023.
- ↑ "Astronauts Christina Koch and Jessica Meir: The 100 Most Influential People of 2020". Time. Archived from the original on March 28, 2025. Retrieved September 23, 2020.
Hanyoyin Haɗi na Waje
[gyara sashe | gyara masomin]| Wikimedia Commons tana da kafofin watsa labarai masu alaƙa da Christina Koch. |
- Christina Koch on IMDb
- Christina H Koch on Twitter

- Christina Koch on Instagram
- 5 Things You Didn't Know About Astronaut Christina Koch – NASA Johnson Space Center, March 13, 2019
- NASA biography
- Appearances on C-SPAN
- CS1 Turanci-language sources (en)
- CS1 Holanci-language sources (nl)
- Commons category link from Wikidata
- AC with 0 elements
- Haifaffun 1979
- Rayayyun Mutane
- 'Yan sama jannati na Artemis
- Masu tafiya a sararin samaniya
- Mutanen Jami'ar Johns Hopkins
- 'Yan Wikimedia na Amurka
- Mutanen da suka yi tafiya a kusa da Wata
- Artemis II
- Pages with reference errors