Christophe Joseph Marie Dabire
Christophe Joseph Marie Dabire | |||
---|---|---|---|
24 ga Janairu, 2019 - 8 Disamba 2021 ← Paul Kaba Thieba (en) - Lassina Zerbo → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | French Upper Volta (en) , 27 ga Augusta, 1948 (76 shekaru) | ||
ƙasa | Burkina Faso | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Lomé University of Bordeaux (en) University of Lille (en) | ||
Harsuna | Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai tattala arziki | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Congress for Democracy and Progress (en) |
Christophe Joseph Marie Dabiré. (an haife shi 27 ga Agustan shekarar 1948) ɗan siyasan Burkina Faso ne wanda ya yi aiki a matsayin Firayim Minista na Burkina Faso daga 24 ga Janairu 2019 zuwa 9 ga Disamban shekarata 2021. Shugaban ƙasar Roch Marc Christian Kaboré ne ya nada shi a matsayin Firaminista bayan murabus din Paul Kaba Thieba da majalisar ministocinsa. Dabiré ya kuma taba wakilci Burkina Faso a kungiyar tattalin arziki da hada-hadar kudi ta yammacin Afirka, sannan ya ci gaba da rike mukamin minista a karkashin, tsohon shugaban kasar Blaise Compaore daga 1994 zuwa 1996, inda Kaboré ke rike da mukamin Firayim Minista.
Sana'a,
[gyara sashe | gyara masomin]Dabiré ya yi aiki a karkashin Thomas Sankara a matsayin daraktan nazari da ayyuka a ma’aikatar tattalin arziki da tsare-tsare daga shekarar 1984 zuwa 1988, lokacin da ya zma babban daraktan hadin gwiwa a ma’aikatar tattalin arziki da tsare-tsare.Ya rike wannan mukamin har zuwa shekarar 1992.
A shekara ta 1992, Dabire ya jagoranci Ma'aikatar Lafiya, har zuwa 1997 lokacin da yake da alhakin Sashen Sakandare, Ilimi da Nazarin Kimiyya na Burkina Faso, mukamin da zai riƙe har zuwa shekarar 2000. A lokacin ya yi aiki a majalisar dokokin Burkina Faso a matsayin mamba na jam'iyyar Congress for Democracy and Progress Party. Bayan da aka sake zaɓe shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a shekarar 2002, Dabiré ya sake yin wani wa'adin shekaru biyar wanda ya ƙare a 2007. An nada shi a matsayin Firayim Minista a ranar 21 ga Janairun shekarar 2019, kuma ya hau mulki bayan kwanaki uku.
A ranar 8 ga Disamban shekarata 2021, yayin da ake fama da rikicin tsaro, shugaban Burkina Faso, Roch Kaboré, ya kori Dabiré a matsayin Firayim Minista. Dokar shugaban kasar ta ce mambobin gwamnatin mai barin gado ne za su gudanar da mulkin kasar har sai an kafa sabuwar gwamnati.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Political offices | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |