Christopher Stephen Ekpenyong
![]() | |||
11 ga Yuni, 2019 - - Godswill Obot Akpabio → District: Akwa Ibom North-West Senatorial District | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Obot Akara, 2 Satumba 1954 (71 shekaru) | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Ƴan uwa | |||
| Abokiyar zama | Grace 19 ga Augusta, 2019) | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
Kensington University (en) Kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya Bida | ||
| Sana'a | |||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party | ||
Christopher Stephen Obong Ekpenyong (
Listen ; haife 29 Satumba 1954) ɗan siyasan Najeriya ne kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Akwa Ibom . [1] An zabe shi a matsayin dan majalisar dattawan Najeriya a 2019 don wakiltar yankin Akwa Ibom ta arewa maso yamma .
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1960, ya halarci makarantar firamare ta St. Patrick, Ikot Ukana kafin ya tafi makarantar firamare ta St. Michael da ke Rumuomasi, a Fatakwal inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko (FSLC). A shekarar 1970 ya halarci Kwalejin Fasaha ta Gwamnati da ke Fatakwal sannan a 1975 ya halarci Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Yaba. A 1977, ya halarci Federal Polytechnic, Bida kuma ya sami Difloma ta Ƙasa da Ƙasa akan Electrical/Electronic Engineering . A cikin shekarar 1980, Ekpenyong ya halarci Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Calabar don samun Difloma ta Ƙasa a Injiniya da Lantarki kuma ya kammala a shekarar 1982.
A cikin shekara ta 1993, ya halarci Jami'ar Kensington, Honolulu, Hawaii, Amurka kuma ya sami digiri na Master of Business Administration (Marketing) a shekarar 1995. Ya sami Doctor of Philosophy daga wannan cibiyar. [2]
Sana'ar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ekpenyong ya kasance mataimakin gwamna a zamanin Gwamna Victor Attah daga shekara ta 1999 zuwa 2005.
A shekarar 2005, ya kafa tarihi a Najeriya: an tsige shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar Akwa Ibom amma sai aka yi gaggawar mayar da shi wannan mukamin cikin ƙasa da kwanaki bakwai. ‘Yan majalisar dokokin jihar sun sauya sheka ne bayan da shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya shiga tsakani, duk da cewa an tilasta wa Ekpenyong yin murabus daga mukaminsa. [3]
A shekarar 2019, an zaɓe shi a matsayin sanata mai wakiltar Akwa Ibom Arewa maso Yamma Sanata a ƙarƙashin jam'iyyar Peoples Democratic Party inda ya doke abokin takararsa mai ci Godswill Akpabio na jam'iyyar All Progressive Congress . Ya samu kuri'u 118,215 sabanin 83,158 na Godswill Akpabio . Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) Peter Ogban ne ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen. [4]
A ranar 9 ga watan Nuwamban shekarar 2019, kotun ɗaukaka ƙara dake Calabar, jihar Cross Rivers, ta bada umurnin sake gudanar da zaɓen sanata a karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom.
A zaɓen Sanatan Akwa Ibom Arewa-maso-Yamma, dan takarar PDP, Chris Ekpenyong, ya samu ƙuri'u’u 134,717 inda ya doke tsohon Sanata Godswill Akpabio, wanda ya samu kuri’u 83,820, bisa ga sakamakon da INEC ta fitar da safiyar Lahadi
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 19 ga Agusta 2019, ya rasa matarsa, Grace Ekpenyong.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Thabit, Khadijah (6 December 2016). "Sorry, we don't want to be part of Biafra – Niger Delta chieftain issues warning to agitators". Legit.ng. Retrieved 9 September 2024.
- ↑ "Profile: Engr. Dr. Obong Chris Ekpeyong – Great Achievers World". Archived from the original on 23 March 2019. Retrieved 18 March 2019.
- ↑ Asadu, Chinedu (26 February 2019). "CLOSE-UP: Chris Ekpenyong, the man who snookered Akpabio". TheCable. Retrieved 9 September 2024.
- ↑ Nnamdi, Onyirioha (26 February 2019). "Breaking: Akpabio loses senatorial seat in Akwa Ibom to PDP's candidate". Legit.ng. Retrieved 9 September 2024.
