Jump to content

Cibiyar Tunawa da Kisan kiyashi ta Murambi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Makarantar Fasaha ta Murambi, wacce yanzu akafi sani da Cibiyar Tunawa da Kisan kiyashi ta Murambi , tana kusa da garin Murambi a kudancin kasar Rwanda.

Wannan Cibiyar Tunawa da kisan kiyashin tana ɗaya daga cikin manyan cibiyoyi shida a Rwanda waɗanda ke tunawa da kisan kare dangi na shekarar 1994 a kan Tutsi a Rwanda . Sauran sune Cibiyar Tunawa da Kigali, Cibiyar Tunawa da Ntarama da sauransu a Cibiyar Tunawar Kisan kiyashi ta Nyamata, Cibiyar Tunawa da Bisesero da Nyarubuye .

gawawwakin wadanda aka kashe a kisan kare dangi. 2001
Wadanda aka kashe a kisan kare dangi.

Wannan shi ne wajen da akayi kisan kiyashi a lokacin kisan kiyashin Rwanda na shekarar 1994. Lokacin da kisan ya fara, Ƙabilar Tutsi a yankin sun yi ƙoƙari su ɓoye a wani coci na yankin. Ko da yake, bishop da magajin gari sun yaudare su zuwa cikin tarko ta hanyar aika su zuwa makarantar fasaha, suna da'awar cewa sojojin Faransa za su kare su a can. A ranar 16 ga Afrilu, 1994 matasan Tutsis 65,000 sun yi tafiya zuwa makarantar. Yayin da wadanda abin ya shafa suka isa sai suka tarar ba a samar da ruwa ko abinci ba. An yi haka ne don a tabbatar da cewa mutane sun raunana sosai tayan da ba zasu iya jurewa ba. Bayan kare kansu na 'yan kwanaki ta amfani da duwatsu, an mamaye Tutsi a ranar 21 ga Afrilu.

Sojojin Faransa sunyi ɓatan-dabo kuma 'yan bindiga na Hutu Interahamwe sun kai hari makarantar. An kashe kimanin ƙabilar Tutsi 20,000 a makarantar, kuma kusan duk wadanda suka tsere an kashe su washegari lokacin da suka yi kokarin ɓoyewa a cikin cocin da ke kusa.[1] Adadin wadanda suka mutu kusan 50,000 da gwamnati ta bayar ba su da goyon baya ga yawan gawawwakin da aka tono, har ma da la'akari da cewa har yanzu ba a bude kaburbura da gawawwakinsa da ba a binne su ba.[2] A cewar wata manuniyar a wurin tunawa; Faransa sun kawo kayan aiki masu nauyi don haƙa ramuka da yawa inda aka sanya dubban gawawwaki acikin daga bisani sai suka sanya kotun volleyball a kan kaburbura domin ƙoƙarin ɓoye gaskiyar abin da ya faru. Daga cikin gawarwakin da ake nunawa a halin yanzu akwai na yara da jarirai.[ana buƙatar hujja]

Mutane 34 ne kawai aka yi zaton sun tsira daga kisan kiyashi na Murambi.

An samar da cibiyar Tunawar a ranar 21 ga Afrilu 1995. Wajen ya ƙunshi kaburbura 50,000. Ginin makarantar yanzu gidan kayan gargajiya ne na kisan kare dangi wanda ke nuna kwarangwal da gawawwakin wasu daga cikin dubban mutane da aka kashe a lardin Gikongoro a shekarar 1994. A cikin binciken shi game da cibiyar tunawa da kisan kare dangi na Rwanda, Timothy Longman ya yi iƙirarin cewa duk dayake an gabatar da gawarwakin da aka nuna a Murambi a matsayin na mutanen da aka kashe a wurin, a zahiri gawarwakin ne da aka kawo Murambi daga ko'ina cikin yankin da ke kewayen wajen, su asalin Wadanda aka kashe a Murambi an binne su a cikin manyan kaburbura a wurin a shekarar 1996.

  1. "Numbers (HRW Report - Leave None to Tell the Story: Genocide in Rwanda, March 1999)". www.hrw.org. Retrieved 2022-03-31.
  2. "Through A Glass Darkly". maps.cga.harvard.edu. Archived from the original on 2022-05-30. Retrieved 2022-04-04.