Clara Bohitile
1995 - 2005 | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Windhoek, 19 Nuwamba, 1955 (70 shekaru) | ||
| ƙasa | Namibiya | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa da Manoma | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | SWAPO | ||
Clara Gasebewe Bohitile (an haife ta a ranar 19 ga watan Nuwamba 1955) 'yar kasuwa ce ta Namibiya kuma tsohuwar 'yar siyasa.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Bohitile a ranar 19 ga watan Nuwamba 1955 a Windhoek. [1] Ta halarci Makarantar Katolika a Tsohuwar Wuri (Old Location), [2] Yankin baƙar fata mazauniyar Windhoek har zuwa ƙarshen shekarar 1950s. Ta kuma yi makaranta a Gunichas Roman Catholic School kusa da Gobabis da kuma makarantar sakandare ta Katolika a Döbra. Bohitile ta sami ilimin tattalin arziki na gida akan manyan makarantu a Kwalejin Tshiye da Jami'ar Vista, duka a Afirka ta Kudu. Bayan ta kammala ta koyarwa a makarantar sakandare ta Immanuel Shifidi ta Windhoek. [3] Ta kuma fara aikin noma kuma ta shiga siyasa.
Aikin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Memba na SWAPO, Bohitile ta kasance memba na Majalisun Ƙasa na 2 da na 3 daga shekarun 1995 zuwa 2005. Ta kuma riƙe muƙamin mataimakiyar ministar ilimi da al'adu daga shekarar 1995 zuwa 2005 kuma. [4] Ta sake shiga majalisar daga shekarun 2007 zuwa 2010 lokacin da ta maye gurbin Ben Amathila, wanda ya yi ritaya. Ita ma memba ce a kwamitin tsakiya na SWAPO.[5]
Sana'ar kasuwanci
[gyara sashe | gyara masomin]Bohitile kuma fitacciyar manomiya ce ta kasuwanci kuma 'yar siyasa. A cikin shekarar 2006, Ƙungiyar Aikin Noma ta Namibia ta ba ta lambar yabo ta Gwarzuwar Manomiyar Shekara. A cikin watan Satumba 2010, ta kafa tarihi lokacin da aka zaɓe ta a hukumar MeatCo Namibia. Ita ce mace ta farko da ta taɓa zama a kujeran hukumar MeatCo. Bohitile kuma tayi aiki a hukumar Windhoek Country Club da Casino.[6]
Karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]An ba Bohitile Kyautattun Excellent Order of the Eagle a Ranar Jarumai ta 2014.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Reporter, New Era (2007-06-13). "A Farmer Among the Best". New Era Live (in Turanci). Retrieved 2019-10-02.
- ↑ Kangueehi, Kuvee. "Namibia: A Farmer Among the Best".[dead link]
- ↑ "Immanuel Shifidi Secondary students engage with FLON and Irish Minister through #Befree". UNFPA Namibia (in Turanci). 2019-04-29. Retrieved 2019-10-02.
- ↑ "Bohitile G. Clara". www.parliament.na. Archived from the original on 2021-04-18. Retrieved 2019-10-02.
- ↑ Clara Bohitile Archived 2011-06-11 at the Wayback Machine Namibia Institute for Democracy
- ↑ Bohitile to chair Meatco Board The Namibian, 3 September 2010
- ↑ "Namibians honoured by President". New Era. 28 August 2014. Archived from the original on 29 June 2018. Retrieved 21 November 2017.