Cutar dake yadu wa ta iska

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wikidata.svgCutar dake yadu wa ta iska
Sneeze.JPG
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na infectious disease (en) Fassara
Has immediate cause (en) Fassara airborne transmission (en) Fassara

Cututtuka da yawa suna yaduwa ne ta hanyar Iska inda kwayoyyi cutar su kan bi Iska ne domin su yadu.[1] Irin wadannan cututtukan suna da mutukar tasiri a fanin kiwon lafiyar Dan Adam da kuma dabbobi. Kwayoyin cutar za su iya zama kwayar halittar virus, bacteria ko kuma gansakuka. Akan yada su ne ta hanyar numfashi, magana, tari, atishawa ko kuma tada kura, feshin magunguna ko kuma sinadaren wanke bandaki.

A mafi yawan lokuta kwayoyin cutar na kawo gyanbo a cikin hanci, makogwaro ko kuma hunhu inda suke jawo tari, toshewar numfashi, ciwon makogwaro da kuma wasu matsalolin a jiki.

Cutar kyanda

Cututtuka da yawa akan kamu da su ne  ta hanyar Iska misali Corona virus, kyanda, bakon dauro, Yan rani[2],sarkewar numfashi, ciwon tarin fuka ko mura da mashako.[3] Mafi yawancin wadannan cututuka na bukatar amfani da naurar ventilator wajen jinyar su.

A Fayyace[gyara sashe | gyara masomin]

Wayar da kai akan zazzabi mai zafi

Cututtukan da muke kamuwa dasu ta hanyar gurbatacciyar Iska wadda ke dauke da kwayoyin cuta akan same su ne idan gurbatacciyar Iska dauke da kwayoyin cutar daga Mara lafiya ta hadu da mutum mai lafiya, ko kuma yawun sa, ko najasar sa, ko atishawar sa dauke da yawu ta fada kan mai lafiya. Misali, atishawa daga Gaban  motar bus ta kan Isa har bayan motar.[4]

Shakar kwayoyin cuta ta hanyar numfashi kan jawo rurucewar hanyar shakar Iska inda hakan ka jawo matsalar numfashi.Yawncin cututtukan numfashi na Dan Adam ba shakar sinadarai ne ke kawo su ba amma kuma hankan na tasiri wajen matsalar numfashi kamar cutar sarke war numfashi watau cutar Asthma.[5]

Cuttukan da ke yaduwa ta Iska kan shafi dabbobin gida kamar su kaji, agwagi, talotalo. Misali cutar Newcastle ta tsuntsaye.[6]

Yada Cutar[gyara sashe | gyara masomin]

Akan kamu da cuta ne Idan mai lafiya ya shaki sinadari, ko ya shiga idanuwan sa ko hancin sa ko bakin sa [7] [8] . Ba wai sai mai lafiya yayi cudanya da Mara lafiya gaba  da ga ba, amma  yanayi na zafi ko laima ko rashin wadatacciyar Iska duk sukan sa a kamu da cutar numfashi [8] .

 • Yaduwar cuta ta hanyar Iska tafi yawa a birni fiye da kauyuka.[3]
 • Yanyin samun mutum bashi da tasiri akan kamuwa da cuta.[9]
 • Zama a kusa da gulbi,tafki,ko rafi na da tasiri wajen yaduwar cutar.[2]
 • Rashin ingancin na'urar sanyaya daki na kara tasirin kamuwa da cuta.[10]
 • A lokuta da yawa rashin tsaftar muhalli a asibiti na haifar da yaduwar annoba.

Riga Kafi[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu daga cikin hanyoyin Riga kafi sune yin allurar lamba ko kuma Riga kafin cutar, sa takunkumi na fuska, da kuma yin nesa da Wanda ya kamu da cutar. Yin cudanya da mai cuta ba dole ne yasa mutum ya harbu ba. Kamuwa da cutar ta hangar Iska ya danganta da karfin garkuwan jiki da mutum yake dashi ko kuma yawan kwayoyin cutar da mutum ya shaka.[11]

Akan yi amfani da magungunan  kashe cututtuka wajen maganin cutar sanyi ta sarkewar numfashi ko ciwon madaukai.[12]

Da yawa daga cikin masana kiwon lafiya sun bada shawarar yin nesa da juna a matsayin hanyar rage kamuwa da cutar da Iska ke yadawa.[13]

Za a iya rage kamuwa da cututtukan da Iska ke yada wa ta hanyar daukar wadannan matakai:

 • Yin nesa da masu cutar
 • Sanya takunkumi a lokacin da za a Shiga taron jama'a
 • Rufe Baki da gwiwar hannu duk lokacin da za a yi tari ko atishawa.
 • Wanke hannuwa kamar na dakika ashirin akai akai.

kada a rika yawan taba  Baki  ko hanci ko idanuwa da hannu ko kuma yin musabiha ko gaisuwar hannu ko sumbatar jama'a.[14]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. Siegel JD, Rhinehart E, Jackson M, Chiarello L, Healthcare Infection Control Practices Advisory Committee. "2007 Guideline for Isolation Precautions: Preventing Transmission of Infectious Agents in Healthcare Settings" (PDF). CDC. p. 19. Retrieved 7 February 2019. Airborne transmission occurs by dissemination of either airborne droplet nuclei or small particles in the respirable size range containing infectious agents that remain infective over time and distance
 2. 2.0 2.1 Pica N, Bouvier NM (2012). "Environmental Factors Affecting the Transmission of Respiratory Viruses". Curr Opin Virol. 2 (1): 90–5. doi:10.1016/j.coviro.2011.12.003. PMC 3311988. PMID 22440971.
 3. 3.0 3.1 497–507. [./Https://en.wikipedia.org/wiki/CiteSeerX%20(identifier) CiteSeerX] 10.1.1.487.177. doi:10.1017/s0953756204001777. PMID 15912938.
 4. https://www.chicagotribune.com/opinion/ct-xpm-2014-04-19-ct-sneeze-germs-edit-20140419-story.html
 5. "Airborne diseases". Archived from the original on 28 June 2012. Retrieved 21 May 2013.
 6. Mitchell, Bailey W.; King, Daniel J. (October–December 1994). "Effect of Negative Air Ionization on Airborne Transmission of Newcastle Disease Virus". Avian Diseases. 38 (4): 725–732. doi:10.2307/1592107. JSTOR 1592107.
 7. "CT provides best diagnosis for COVID-19". ScienceDaily. Retrieved 14 March2020.
 8. 8.0 8.1 Ai T, Yang Z, Hou H, Zhan C, Chen C, Lv W, et al. (February 2020). "Correlation of Chest CT and RT-PCR Testing in Coronavirus Disease 2019 (COVID-19) in China: A Report of 1014 Cases". Radiology: 200642. doi:10.1148/radiol.2020200642. PMID 32101510.
 9. Peternel R, Culig J, Hrga I (2004). "Atmospheric concentrations of Cladosporium spp. and Alternaria spp. spores in Zagreb (Croatia) and effects of some meteorological factors". Ann Agric Environ Med. 11 (2): 303–7. PMID 15627341.
 10. "Legionnaire disease". Retrieved 12 April 2015.
 11. Laura Ester Ziady; Nico Small (2006). Prevent and Control Infection: Application Made Easy. Juta and Company Ltd. pp. 119–120. ISBN 9780702167904. Retrieved 21 May 2013.
 12. "Redirect - Vaccines: VPD-VAC/VPD menu page". 7 February 2019.
 13. Glass RJ, Glass LM, Beyeler WE, Min HJ (November 2006). "Targeted social distancing design for pandemic influenza". Emerging Infect. Dis. 12 (11): 1671–81. doi:10.3201/eid1211.060255. PMC 3372334. PMID 17283616.
 14. Pietrangelo Ann. What Are Airborne Diseases? Healthline 19 March 2020.. Accessed on 13 April 2020