Dévote Faida
| |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa |
Kirundo (mul) | ||
| ƙasa | Burundi | ||
| Karatu | |||
| Harsuna |
Kirundi (en) Turanci Faransanci Harshen Swahili | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
Dévote Faida (an haife ta a shekara ta 1983) 'yar siyasa ce wacce aka zaɓa Sanata na Lardin Kirundo, Burundi a shekarar 2020.
Sanata
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 28 ga watan Yuli, 2020 Kotun Tsarin Mulki ta Burundi ta tabbatar da cewa an zaɓi Devote Faida a matsayin 'yar majalisar dattawa a matsayin wakiliyar Hutu na lardin Kirundo. Ta yi takara a dandalin National Council for the Defence of Democracy - Forces for Defence of Democracy (CNDD-FDD) . [1] An naɗa Dévote Faida a matsayin shugabar zaunannen kwamiti mai kula da al'amuran jinsi da hulɗa da majalisar dokoki na kungiyar ƙasashen gabashin Afrika. [2]
A ranar 30 ga watan Nuwamba, 2021, ta rufe taron musayar ra'ayi da tantance tsarin yaki da aurar da yara ƙanana da cikin shege ga ɗalibai, a babban birnin lardin Karuzi. An kuma gudanar da zama a Ngozi, Rutana da kuma birnin Bujumbura. [2] Majalisar dattawan kasar Burundi ce ta shirya taron bitar tare da goyon bayan hukumar kare hakkin ɗan adam ta ƙasa CNIDH da asusun kula da yara na majalisar ɗinkin duniya UNICEF. [3] An ba da shawarwari ga majalisar dattawan Burundi, gwamnati, da kuma hukumomin shari'a, ilimi da na addini. [2]
A ranar 8 ga watan Satumba, 2023 mambobin kwamitin dindindin da ke kula da batutuwan da suka shafi jinsi da dangantaka sun gana a majalisar dattawan Burundi tare da shugabannin hukumomin larduna daban-daban, da nufin tattara bayanai dangane da cin zarafin mata. A matsayinta na shugaban hukumar, Dévote Faida ta yi kira ga dukkan mahalarta taron da su haɗa kai don kawar da wannan annoba. [4]