Jump to content

Aliyu Idris Funtua

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aliyu Idris Funtua
Rayuwa
ƙasa Funtua
Sana'a

Dakta Aliyu Idris Funtua shehin malamin boko ne kuma shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Katsina, Jihar Katsina. Ya zama shugaba na 13 da ya riƙe wannan muƙamin a kwalejin, biyo bayan samun amincewar Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 19 ga watan agustan shekarar, 2016[1][2][3] Ko kafin wannan nadi, shi ne mataimakin shugaban Kwalejin kuma mai rikon kwarya. A shekarar 2020 ne aka sake sabunta muƙaminsa na Shugaban Kwalejin Ilimi ta Katsina. Shi dai Dakta Aliyu Idris Funtua na da digirin digirgir daga Jami'ar Bayero ta jihar Kano wanda ya samu a shekara ta 2016.[4].[Ana bukatan hujja]

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Dakta ya fito ne daga Karamar Hukumar Funtua da ke Jihar Katsina. Mai Marbata Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman ya ba Dakta Aliyu Idris Funtua sarautar 'Wakilin Malaman Katsina' a shekarar, 2018. Wannan na daga cikin sarautun da yake da su.[5]

Shi dai Dakta an haifeshi ne a garin Dandume a shekarar, 1962 amma ya taso ne a garin Funtua inda yayi firamare ta Aya watau (Aya Primary School) a garin na Funtua sai yayi makarantar gaba da piramare a garin Malumfashi. Ya samu shedar Malanta daga Kwalejin Ilmi ta Katsina a shekarar, 1984. A Jami'ar Bayero ta Kano ne ya yi karatun digirinsa na farko da na biyu da na uku a Kimiyyar Harshen Hausa.[6]

Bayan koyarwa da yayi a Makarantar Sakandare ta Gwamnati dake Gwoza a tsakanin shekarar, 1984 zuwa 1985, Malam Aliyu idris Funtua ya fara aiki da Jihar Kaduna ta da a matsayin malamin kuma ya riƙe mukamai daban-daban har zuwa shekarar, 1997 lokacin da ya zama mataimakin shugaban makarantar sakandare.

Likkafa ta ci gaba a lokacin da Dakta Funtua ya zama malamin kwaleji a shekara ta, 1997 kuma ci gaba da bada gudunmuwarsa a fagen da ya kware da kuma riƙe mukamai daban-daban.[5] Bayan samar da Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Katsina, an ɗauki aron Dakta inda ya koyar tun daga shekarar, 2009 zuwa 2010. A shekarar, 2011 ne Dakta ya kai matakin Babban Laccara watau (Chief Lecturer).[5]

Dakta Aliyu Idris Funtua na da iyali da yara.[7][8]

  1. https://dailytrust.com/fce-obudu-provost-assumes-work/
  2. Webmaster (2016-08-26). "FCE Katsina gets new provost". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-02-20.
  3. "FCE Katsina, Obudu get new provosts | The Nation Newspaper". The Nation Newspaper. (in Turanci). 2016-08-26. Retrieved 2023-02-20.
  4. Webmaster (2016-09-01). "FCE Obudu provost assumes work". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-03-04.
  5. 5.0 5.1 5.2 Mustapha, Olusegun (2018-04-13). "Dokta Aliyu Funtuwa ya zama wakilin Malaman Katsina". Aminiya (in Turanci). Retrieved 2023-02-20.
  6. https://thesourcereporters.wordpress.com/2022/11/05/dr-aliyu-idris-six-years-on-the-saddle/
  7. "Buhari Appoints Two New Provosts for FCEs Obudu, Katsina – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2023-02-24.
  8. https://www.thisdaylive.com/index.php/2016/08/26/buhari-appoints-two-new-provosts-for-fces-obudu-katsina/